Babban Labari

An zaɓi Tinubu a matsayin sabon shugaban ECOWAS

An zaɓi Tinubu a matsayin sabon shugaban ECOWAS

An zaɓi Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu a matsayin sabon Shugaban Ƙungiyar Raya Tattalin Arzikin Ƙasashen Yammacin Afirka (ECOWAS). Wannan ya faru ne yayin taron ƙungiyar karo na 63 wanda ya gudana a Guinea Bissau a ranar Lahadi. Wannan ne karo na farko da Tinubu ya halarci taron na ECOWAS tun bayan rantsar da shi a ranar 29 ga watan Mayun 2023. A makon jiya ne Shugaba Tinubu ya karɓi bakuncin Shugaba Embalo a birnin Legas, inda ya ce sun ci abinci tare kuma “mun tattauna kan batutuwa da dama da suka shafe mu.” A wancan lokacin, Tinubu ya ce…
Read More
Tinubu bai fitar da jerin sunayen ministoci ba – Fadar Shugaban Ƙasa

Tinubu bai fitar da jerin sunayen ministoci ba – Fadar Shugaban Ƙasa

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja A ranar Alhamis Fadar Shugaban Ƙasa ta bayyana cewa, ba a kammala shirya jerin sunayen ministocin da Shugaba Bola Ahmed Tinubu zai naɗa ba. Mataimakin Musamman ga Shugaban Ƙasa kan ayyuka na musamman, sadarwa da dabaru, Dele Alake, ne ya bayyana haka a yayin ganawa da manema labarai a fadar gwamnati da ke Abuja. Alake ya buƙaci ‘yan Nijeriya da su yi watsi da jita-jitar da ke tattare da jerin sunayen ministocin da ake jira. "Game da jerin ministocin, babu gaskiya a cikin duk waɗannan abubuwan," inji Alake. "Lokacin da Shugaban Ƙasa ya natsu…
Read More
Ba zan wahalar da ’yan Nijeriya kamar gwamnatin Buhari ba – Tinubu

Ba zan wahalar da ’yan Nijeriya kamar gwamnatin Buhari ba – Tinubu

*Ya rage harajin da aka ƙaƙaba na shigo da motoci da sauransu  Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Shugaban Nijeriya, Bola Ahmed Tinubu, ya sauya wasu harajin da aka sanya a cikin mintunan ƙarshe da tsohon Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari, wanda ya rattava wa hannu, yana mai cewa ba zai shaƙe ‘yan Nijeriya ya wahalar da su kamar yadda gwamnatin baya ta yi ba. Shugaban ya soke harajin ne a cikin umarnin zartarwa a jiya Alhamis, 6 ga Yuli, 2023. Harajin sun haɗa da dakatar da harajin kashi 5 da ake cece-kuce kan ayyukan sadarwa; Harajin Kore na kashi 10…
Read More
Rahoton EU: Atiku da Obi sun yi ca a kan Tinubu

Rahoton EU: Atiku da Obi sun yi ca a kan Tinubu

Daga BASHIR ISAH 'Yan takarar shugaban ƙasa, Atiku Abubakar na Jam'iyyar PDP da Peter Obi na Jam'iyyar Labour a zaɓen 2023 da ya gabata, sun yi ca a kan Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu, na ƙin yarda da rahoton ƙarshe da Ƙungiyar Tarayyar Turai (EU) ta fitar kan zaɓen shugaban ƙasa da ya gudana a ranar 25 ga Fabrairun da ya gabata. A ranar Talata, 27 ga Yuni, EU ta miƙa rahoton nata game da zaɓen a Abuja. Babban jami'in sanya ido, Barry Andrews, ya ce rahoton ya samo asali ne daga nazarin bin ƙa’idojin da Nijeriya ta ɗauka na…
Read More
Tinubu ya yi watsi da rahoton Tarayyar Turai kan zaɓen 2023

Tinubu ya yi watsi da rahoton Tarayyar Turai kan zaɓen 2023

Daga BASHIR ISAH Fadar Shugaban Ƙasar Nijeriya ta yi watsi da rahoton da Ƙungiyar Tarayyar Turai (EU) ta fitar kan babban zaɓen 2023 da ya bai wa Asiwaju Bola Ahmed Tinubu na Jam'iyyar APC damar zama Shugaban Nijeriya. Cikin Sanarwar da Mai Bai wa Shugaban Ƙasa Sahwara Kan Ayyuka na Musamman, Sadarwa da Tsare-tsare, Mr Dele Alake, ya fitar a ranar Lahadi, Fadar ta ce babu gamsassun hujjoji da ƙungiyar ko danginta suka bayar da za su iya ƙalubalantar sahihancin sakamakon babban zaɓen na 2023. A cewar Alake, rahoton Ƙungiyar Tarayyar Turan rahoto ne mara inganci wanda aka shirya shi…
Read More
Shugaban Guinea-Bissau ya ziyarci Tinubu

Shugaban Guinea-Bissau ya ziyarci Tinubu

Daga BASHIR ISAH Shugaban Ƙasa Bola Tinubu ya karɓi baƙuncin takwaransa na ƙasar Guinea-Bissau, Umaro Sissoco Embalo, a Legas. Embalo, wanda jigo ne a ƙungiyar ECOWAS, ya ziyarci Tinubun ne a ranar Asabar. Shugaba Tinubu ya yi hutun sallah ne a Legas tun bayan da ya dawo daga London a ranar Talata. Embalo ya zama Shugaban Ƙasa a Afirka na farko da ya ziyarci Tinubu tun bayan da aka rantsar da shi a matsayin Shugaban Nijeriya na 16 a ranar 29 ga Mayu, 2023.
Read More
Babbar Sallah: Yadda Shugaba Tinubu ya halarci Sallar Idi

Babbar Sallah: Yadda Shugaba Tinubu ya halarci Sallar Idi

Daga BASHIR ISAH Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya bi sahun al'ummar musulmin duniya wajen gabatar da Sallar Idi ta Babbar Allah wadda aka yi a ranar Laraba, 10 ga watan Zul-Hijja wanda ya yi daidai da 28 ga watan Yunin 2023. Tinubu ya yi Sallar Idinsa ne a filin Idi da ke Obalende a Dodan Barracks, Victoria Island, Legas. Imam Suliman Abuo-Nolla shi ne wanda ya jagoranci gabatar da sallar mai raka'o'i biyu. Ga ƙarin hotuna:
Read More
An yi wa Shugaban Ƙasa da gwamnoni ƙarin albashi da kashi 114

An yi wa Shugaban Ƙasa da gwamnoni ƙarin albashi da kashi 114

Daga BASHIR ISAH Hukumar Tattara da Raba Kuɗaɗen Shiga (RMAFC), ta amince da ƙarin albashi da kashi 114 ga manyan jami'an gwamnati. Waɗanda ƙarin albashin ya shafa sun haɗa da Shugaban Ƙasa da Mataimakinsa, gwamnoni, 'yan majalisu, ma'aikatan shari'a da sauransu. RMAFC ita ce hukumar da ke tantance albashin da ake yanka wa 'yan siyasa da sauran masu riƙe da muƙaman siyasa, ciki har da Shugaban Ƙasa, Mataimakin Shugaban Ƙasa, Gwamnoni da sauransu kamar yadda Sashe na 84 da 124 na Kundin Tsarin Mulki ya nuna. Shugaban RMAFC, Muhammadu Shehu, bisa wakilcin kwamishina a hukumar, Rakiya Tanko-Ayuba, shi ne ya…
Read More
Tinubu ya naɗa Nuhu Ribaɗu da wasu a shugabancin fannin tsaro

Tinubu ya naɗa Nuhu Ribaɗu da wasu a shugabancin fannin tsaro

Daga BASHIR ISAH A ranar Litinin Shugaban Ƙasa sauke duka jami'an da ke jan ragamar fannin tsaron Nijeriya nan take. Kazalika, ba tare da ɓata lokaci ba Tinubun ya amince da naɗin waɗanda za su maye gurbin saukakkun. Waɗanda sabbin naɗe-naɗen ya shafa sun haɗa da: 1 Malam Nuhu Ribadu, Mai wa Shugaban Ƙasa Shawara Kan Sha'anin Tsaro2 Manjo Janar C.G Musa, Babban Hafsan Tsaro3 Manjo T. A Lagbaja, Babban Hafsan Sojoji4 Rear Admirral E. A Ogalla, Babban Hafsan Sojojin Ruwa5 AVM H.B Abubakar, Babban Hafsan Mayaƙan Sama6 DIG Kayode Egbetokun, Muƙaddashin Sufeto-Janar na 'Yan Sanda7 Manjo Janar EPA Undiandeye,…
Read More