Babban Labari

Tinubu ya sauke shugabannin tsaro

Tinubu ya sauke shugabannin tsaro

Daga BASHIR ISAH Shugaban Ƙasa Bola Tinubu ya sauke shugabannin tsaron Nijeriya baki ɗaya. Bayanin haka na ƙunshe ne cikin sanarwar da Daraktan Yaɗa Labarai na Ofishin Sakataren Gwamnatin Tarayya, Willie Bassey, ya fitar a ranar Litinin. Tinubu ya bi bayan sauke jami'an da naɗa sabbin da za su maye gurbinsu. A cewar sanarwar, “Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu, GCFR, ya amince da ritayar dukkan shugabannin tsaro da Sufeto-Janar na 'Yan Sanda, masu ba da shawara da Kwanturola-Janar na Hukumar Kwastam." Sanar ta ƙara da cewa, sauke su ɗin ya fara aiki ne nan take, haka ma waɗanda aka naɗa…
Read More
Cire tallafin mai: An ware tallafin Naira biliyan 702 ga ma’aikata

Cire tallafin mai: An ware tallafin Naira biliyan 702 ga ma’aikata

*Amfani da fetur ya ragu daga lita miliyan 67 zuwa 40 kullum*Tinubu na neman tallafin majalisa don samar da motoci masu lantarki Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Majalisar Tattalin Arziki ta Ƙasa (NEC) ta bayyana a jiya Alhamis cewa, tana duba yiwuwar ware Naira biliyan 702 na kuɗin rayuwa a matsayin tallafu ga ma’aikatan gwamnati a wani ɓangare na matakan daƙile raɗaɗin cire tallafin man fetur. A yayin da ya ke jawabi ga manema labarai a fadar gwamnatin jihar a ƙarshen taron na NEC wanda Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, ya jagoranta, Gwamna Bala Mohammed na Jihar Bauchi ya…
Read More
Da Ɗumi-ɗumi: Tinubu ya dakatar da shugaban EFCC, Bawa

Da Ɗumi-ɗumi: Tinubu ya dakatar da shugaban EFCC, Bawa

Shugaban Ƙasa Bola Tinubu, ya dakatar da Shugaban Hukumar EFCC, AbdulRasheed Bawa, har baba-ta-gani. An dakatar da Bawa ne domin samun damar gudanar da bincike kan zarge-zargen da ake yi masa na yin amfani da ofishinsa wajen aikata ba daidai ba. Sanarwar da Daraktan Yaɗa Labarai na Ofishin Sakataren Gwamnatin Tarayya, Willie Bassey, ya fitar ta ce, an dakatar da Bawa ne saboda zargin da ake yi masa na keta alfarmar ofishinsa. “An umarci Bawa da ya gaggauta miƙa ragamar ofishinsa ga Daranktan Ayyuka a hukumar, wanda shi zai ci gaba da kula da hukumar zuwa lokacin da za a…
Read More
Akpabio ya zama Shugaban Majalisar Dattawa

Akpabio ya zama Shugaban Majalisar Dattawa

Daga BASHIR ISAH An zaɓi ɗan takarar Shugaban Majalisar Dattawa na Jam'iyyar APC, Godswill Akpabio, a matsayin Shugaban Majalisar Dattawa. Akpabio ya lashe zaɓen da ƙuri'u 63 inda ya doke Sanata Abdulaziz Yari wanda ya tsira da ƙuri'u 46. Akawun Majalisar Tarayya, Sani Tambuwal, shi ne ya sanar da sakamakon zaɓen. Tambuwal ya ce sanatoci 107 ne suka kaɗa ƙuri'a. Sanata Ali Ndume ne ya zaɓi Akpabio don takarar Shugaban Majalisar, yayin da Sanata Adeola Olamilekan, daga Jihar Ogun, ya mara masa baya.
Read More
Gabanin zaɓen shugabannin majalisa… A na zargin ƙulla maƙarƙashiyar kama Yari

Gabanin zaɓen shugabannin majalisa… A na zargin ƙulla maƙarƙashiyar kama Yari

*Ƙungiya ta ja hankalin Tinubu da APC*Kotu ta tsawaita wa’adin hana kama shi*Za a ƙaddamar da Majalisa ta 10 ranar Talata Daga NASIR S. GWANGWAZO da MAHDI M. MUH’D Rahotanni sun nuna cewa, jami’an tsaron Nijeriya suna ƙulle-ƙullen kama tsohon Gwamnan Jihar Zamfara, Abdul’aziz Yari, su tsare shi har sai bayan ƙaddamar da Majalisar Dokokin Nijeriya ta 10 da za a yi ranar Talata mai zuwa, don tabbatar da cewa, bai samu damu tsaya wa takarar shugabancin Majalisar Dattawa ba. Wannan zargin ya fito ne daga bakin Shugaban Ƙungiyar Matasan Yankin Arewa Maso Gabas (North East Youth Organisation Forum), Alhaji…
Read More
Cire tallafin mai: Gwamnoni sun yi wa Tinubu mubaya’a

Cire tallafin mai: Gwamnoni sun yi wa Tinubu mubaya’a

Daga BASHIR ISAH Gwamnoni 36 a faɗin ƙasa, sun bayyana goyon bayansu ga Shugaban Ƙasa Bola Tinubu dangane da batun cire taffin mai. Gwamnonin sun bayyana haka ne yayin ganawar da Shugaban Ƙasar ya yi da Ƙungiyar Gwamnoni (NGF), ranar Laraba a fadarsa da ke a Abuja. Gwamnonin ƙarƙashin jagorancin Gwamna AbdulRahman AbdulRazaq na Jihar Kwara, sun bayyana farin ciki da gamsuwarsu game da matakin cire tallafin mai da Shugaba Bola ya ɗauka. Kazalika, sun bai wa Tinubun tabbaci tare da ɗaukar masa alƙawarin za su yi aiki tare a kan haka. Tun farko da yake jawabi, Shugaba Tinubu ya…
Read More
Batun cire tallafin mai ya rikita ƙasa

Batun cire tallafin mai ya rikita ƙasa

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Tun bayan da zaɓaɓɓen sabon Shugaban Nijeriya, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, ya furta kalaman cewa, an kawo ƙarshen biyan tallafin man fetur da Gwamnatin Tarayya ke yi a ƙasar, al’amura suka soma rikicewa, inda kace-nace ya ɓalle kan batun, sannan kayayyaki suka yi mummunan tashin gwauron zabo, wanda ba a tava ganin irinsa ba a nan kusa, musamman ma farashin litar man fetur ya ninka kusan sau uku. Shugaba Tinubu ya yi wannan furuci ne a lokacin da ya ke gabatar da jawabinsa na farko a matsayin Shugaban Ƙasa ranar Litinin, 29 ga Mayu,…
Read More
Cire Tallafin Mai: Farashin fetur ya cilla zuwa N700 kan lita guda

Cire Tallafin Mai: Farashin fetur ya cilla zuwa N700 kan lita guda

Daga BASHIR ISAH Rahotanni daga sassan Nijeriya sun ce, a halin da ake ciki farashin fetur ya ƙaru zuwa Naira 700 kan kowace lita a wasu sassan ƙasar. Wannan ya biyo bayan sanar da cire tallafin mai baki ɗaya da sabon Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya yi a jawbinsa ga ‘yan ƙasa jim kaɗan da rantsar da shi a ranar Litinin da ta gabata. Binciken Manhaja ya gano cewar, matakin cire tallafin da Shugaba Tinubu ya ɗauka ya haifar da ƙarin farashin mai da kashi 100 zuwa 250, inda a yanzu ake sayar da lita guda na fetur tsakanin…
Read More
Ƙarancin mai ya kunno kai sa’o’i bayan da Shugaba Tinubu ya sanar da cire tallafin mai

Ƙarancin mai ya kunno kai sa’o’i bayan da Shugaba Tinubu ya sanar da cire tallafin mai

Da alama layukan ababen hawa a gidajen mai ya dawo a Jihar Legas sa'o'i bayan da Shugaban Ƙasa Bola Tinubu ya sanar da cire tallafin mai. Bayanai sun ce an ga cinkoson ababen hawa a gidajen mai ɗin NNPC a yankunan Ikeja da Alausa waɗanda ke jiran su sha mai. Ya zuwa haɗa wannan labari, an ga da daman gidan mai masu zaman kansu a yankunan ba su sayar da mai. A jawabinsa, Shugaba Tinubu ya ce masu ƙumbar susa kaɗai ke amfna da tallafin mai amma ban da talakawa. Ya ce, “Mun yaba da ƙoƙarin gwamnati mai barin gado…
Read More