Babban Labari

Tinubu ya miƙa wa Buhari hannayen amsar mulki

Tinubu ya miƙa wa Buhari hannayen amsar mulki

*Tinubu ya bada sunayen mutane 13*Buhari ya ɓaro manyan ayyukan Naira tiriliyan 1.535*Buhari zai gadar wa Tinubu shirin maganta matsalar tsaro na shekara biyar Daga SANI AHMAD GIWa da MAHDI M. MUHAMMAD Zaɓaɓɓen Shugaban Ƙasar Nijeriya mai jiran gado, Bola Ahmed Tinubu ya miƙa wa Sakataren Gwamnatin Tarayya Mr. Boss Mustapha sunayen mutane 13 da za su yi aiki da kwamitin miƙa mulki da bangaren gwamnati mai barin gado da take ƙarƙashin jagorancin Shugaba Muhammadu Buhari. Tinubu ya kasance a ranar 1 ga Maris, 2023, aka ayyana shi a matsayin wanda ya lashe zaɓen Shugaban Ƙasa na ranar 25 ga…
Read More
Da Ɗumi-Ɗumi: Gobe take Ƙaramar Sallah a Nijeriya

Da Ɗumi-Ɗumi: Gobe take Ƙaramar Sallah a Nijeriya

Mai Alfarma Sarkin Musulmi ya sanar da cewa ya samu sahihan rahotanni daga sassan ƙasa dangane da ganin watan Ƙaramar Sallah. Don haka idan Allah Ya kai mu gobe Juma'a, take 1 ga watan Shawwal, 1444 AH wanda ya zo daidai da 20 ga Afrilu, 2023. Kwamitin tantance ganin wata ƙarƙashin jagorancin Wazirin Sakkwato, Farfesa Sambo Wali Junaidu ne ya jagoranci aikin tabbatar da ganin watan.
Read More
Hedikwatar INEC ta ƙi amincewa da bayyana Binani a matsayin wadda ta lashe zaɓen Gwamnan Adamawa

Hedikwatar INEC ta ƙi amincewa da bayyana Binani a matsayin wadda ta lashe zaɓen Gwamnan Adamawa

*Ta ba da umarnin dakatar da ci gaba da tattara sakamakon zaɓe Babban Ofishin Hukumar Zaɓe ta Ƙasa, INEC, ya dakatar ta ci gaba da tattara sakamakon zaɓen cike giɓi na Gwamnan Jihar Adamawa da ya gudana ranar Asabar. Ofishin ya ɗauki wannan mataki ne bayan da labarin ayyana 'yar takarar Jam'iyyar APC, Sanata Aisha Dahiru (Binani) a matsayin wadda ta lashe zaɓe da Kwamishinan Zaɓe na jihar, Farfesa Hudu Yunus Ari, ya yi a ranar Lahadi ya isa gare shi. Cikin sanarwar da INEC ta wallafa a shafinta na Tiwita mai ɗauke da sa hannun Kwamishinan hukumar, Barista Festus…
Read More
Sanata Binani ta ɗaɗa Gwamna Fintiri da ƙasa a Adamawa

Sanata Binani ta ɗaɗa Gwamna Fintiri da ƙasa a Adamawa

Hukumar Zaɓe ta Ƙasa, INEC, ta ayyana Sanata Aisha Dahiru (Binani) a matsayin wadda ta lashe zaɓen Gwamnan Jihar Adamawa. Kwamshinan Zaɓe na Jihar Adamwa, Farfesa Hudu Yunus Ari, shi ne ya bayyana nasarar Binani wadda ta kasance 'yar takarar Jam'iyyar APC. Da fari, Gwamna Ahmadu Fintiri na Jam'iyyar PDP ne ke gaba da yawan ƙuri'u kafin daga bisani Binani ta shige gabansa. Magoya bayan jam'iyyar PDP sun nuna rashin jin daɗinsu ganin Kwamishinan Zaɓe na jihar ne ya bayyana sakamakon zaɓen maimakon Baturen Zaɓe. Da wannan nasarar da ta samu, a iya cewa Sanata Aisha ta zamo mace ta…
Read More
Yadda zaɓen cike gurbi na gobe zai iya canja fasalin shugabancin majalisa

Yadda zaɓen cike gurbi na gobe zai iya canja fasalin shugabancin majalisa

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Gabanin sake zaɓen cike gurbi na Majalisar Dokoki ta Ƙasa a gobe, 15 ga Afrilu, 2023, jam’iyyun adawa da ’yan takara, a ƙarshen mako, sun ƙara zage damtse don samun galaba a zaɓen da kuma rage ƙarfin jam’iyyar APC mai mulki a Majalisar Dokokin Ƙasa. Za a cike zaɓen gwamnoni biyu, na sanatoci biyar, na majalisar wakilai 31 da kuma kujeru 57 na jiha. Jam’iyyar APC ce ke da rinjaye a sakamakon zaɓen shugaban ƙasa da na ’yan majalisun tarayya da aka gudanar a ranar 25 ga watan Fabrairu da na 18 ga watan Maris, inda…
Read More
Tinubu a kotu: Atiku ya saba shan kayin zaɓe

Tinubu a kotu: Atiku ya saba shan kayin zaɓe

*Ya roƙi ga ɗan takarar na PDP*Dalilan da suka hana Atiku cin zaɓe, inji Tinubu Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Zaɓaɓɓen Shugaban Ƙasa mai jiran gado, Bola Ahmed Tinubu, ya ce, ɗan takarar Shugaban Ƙasa na Jam’iyyar PDP, Alhaji Atiku Abubakar, a kodayaushe yana shan kayi a yunƙurinsa na neman shugabancin Nijeriya tun shekarar 1993. Don haka sai Tinubu ya roqi Atiku da kada ya kalli rashin nasararsa a zaɓen da ya gabata a matsayin baƙon abu, yana mai cewa, hakan ba zai zama abin al’ajabi ga Jam’iyyar PDP da ɗan takararta idan aka yi la’akari da rikicin da…
Read More
Zargin gwamnatin riƙon ƙwarya: Jam’iyyu sun nemi a yi ’yar ƙure

Zargin gwamnatin riƙon ƙwarya: Jam’iyyu sun nemi a yi ’yar ƙure

*PDP da APC na son DSS ta kama sunaye*Cikin LP ya ɗuri ruwa Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Manyan tawagar ƙungiyoyin yaƙin neman zaɓen Shugaban Ƙasa na jam’iyyun APC da PDP sun ƙalubalanci hukumar tsaro ta farin kaya (DSS) da ta kamo kuma ta bayyana masu shirya gudanar da gwamnatin riƙon ƙwarya a Nijeriya. Majalisar a wata tattaunawa daban-daban da jaridun Nijeriya a ranar Laraba, 29 ga Maris, 2023, a Abuja, ta ce yunƙurin gudanar da gwamnatin riƙon ƙwarya ya saɓa wa kundin tsarin mulkin ƙasar, inda ta ce, ya kamata a gano waɗanda suka shirya maƙarƙashiyar (sunansu) tare…
Read More
Ni na kashe Ummita amma ba da gayya ba, inji Ɗan Chana

Ni na kashe Ummita amma ba da gayya ba, inji Ɗan Chana

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Ɗan ƙasar Chanan nan mai suna Frank Geng Quangrong mai shekaru 47 da ake tuhuma da laifin kashe budurwarsa (Ummita) a jiya Alhamis ya tabbatar wa wata babbar kotu a Kano cewa ya dava wa budurwarsa ‘yar Nijeriya mai suna Ummukulsum Sani wadda aka fi sani da Ummita wuƙa, amma ba da niyyar kashe ta ba, a cewarsa. Wanda ake tuhumar, wanda ke zaune a Railway Quarters Kano, na ci gaba da gurfana ne a gaban kotun bisa laifin kisan kai. Frank da lauyan masu gabatar da ƙara ke yi masa tambayoyi, Darakta mai…
Read More
Gawuna ya taya Abba Kabir murnar lashe zaɓen Gwamnan Kano

Gawuna ya taya Abba Kabir murnar lashe zaɓen Gwamnan Kano

Daga IBRAHIM HAMISU a Kano Ɗan takarar jam’iyyar APC a zaɓen gwamna a jihar Kano, Dakta Nasiru Yusuf Gawuna, ya taya Abba Kabir Yusuf na jam’iyyar NNPP, wanda ya lashe zaɓen da ya gudana a ranar 18 ga watan Maris, murna. Ta cikin wani sako na murya da mai magana da yawunsa, Hassan Musa Fagge, ya saki a manhajar WhatsApp a ranar Laraba, Gawuna ya yi wa Abba Gida-Gida addu’ar Allah Ya sa ya zama shugaba nagari. A cewar Gawuna, tun bayan da hukumar zaɓe, INEC, ta sanar da Abba Kabir Yusuf a matsayin wanda ya lashe zaɓen, jam’iyyar APC…
Read More
Da Ɗumi-ɗumi: Gobara ta tashi a Kasuwar Balogun da ke Legas

Da Ɗumi-ɗumi: Gobara ta tashi a Kasuwar Balogun da ke Legas

Da safiyar Talata aka samu aukuwar gobara a kasuwar wadda ta laƙume wani sashe na kasuwar. Jaridar Premium Times ta rawaito cewar gobarar ta tashi ne a sashen da galibi takalman mata ake sayarwa. Da yake tabbatar da aukuwar iftila'in, hadimin Gwamnan Legas kan harkokin yaɗa labarai, Jubril Gawat, ya ce jami'an kwana-kwana sun dira kasuwar domin kashe gobarar. Sai dai ya zuwa haɗa wannan labari, babu ƙarin bayani a hukumance game da abin da ya haddasa gobarar da kuma asarar da aka tafka a dalilin gobara.
Read More