04
Feb
Daga UMAR M. GOMBE A halin da ake ciki, Cristiano Ronaldo ya zama kan gaba a tarihin duniyar ƙwallon kafa a matsayin wanda ya fi kowane ɗan wasan yawan zira ƙwallo a raga. A cewar Marca, Ronaldo wanda dan asalin ƙasar Portugal ne, ya taki wannan matsayi ne a karawar da ƙungiyarsu ta yi da Inter Milan a daren da ya gabata a wasan kusa da na ƙarshe na cin kofin Italiya. Yadda al’amarin yake yanzu, Ronaldo ya ci ƙwallaye guda 763 a matsayinsa na dan ƙwallo, wanda hakan ya zarce na marigayi Josef Bican da Pele, wanda kowannensu ya…