Wasanni

NFF na shirye-shiryen naɗa sabon kocin Super Eagles

NFF na shirye-shiryen naɗa sabon kocin Super Eagles

Hukumar ƙwallon ƙafa ta Nijeriya, NFF, ta kusa kawo ƙarshen taƙaddamar da ake yi kan zaɓen wanda zai cigaba da jan ragamar horar da ’yan wasan Super Eagles na Nijeriya, duk da cewa har yanzu akwai tsaikon da ake fuskanta kan cire caya daga cikin mutane biyu da suka rage. Tawagar Super Eagles ba ta da koci tun bayan da Finidi George ya ajiye aikinsa bayan wasa biyu kacal a cikin kwatiraginsa ta shekara biyu. Finidi yana cikin ’yan wasan Nijeriya da suka lashe Gasar Cin Kofin Nahiyar Afirka (Afcon) ta shekarar 1994, sannan ya taɓa riƙe matsayin na riƙon…
Read More
Gasar Kofin Duniya: An cire Messi daga cikin waɗanda za su buga wa Argentina wasannin fitar da gwani

Gasar Kofin Duniya: An cire Messi daga cikin waɗanda za su buga wa Argentina wasannin fitar da gwani

Kamfanin Dillancin Labarai na ya bayyana cewa, AP Lionel Messi bai zai buga wa Argentina wasannin fidda gwani na neman gurbin shigar Gasar Kofin Duniya ba saboda raunin da ya ji. Kocin Argentina Lionel Scaloni ya sanar da tawagar ’yan wasa mai qunshe da ’yan qwallo 28 a ranar Litinin. Argentina za ta kara ne da Chile a ranar 5 ga watan Satumba, sai kuma kwanaki biyar bayan hakan ta kara da Colombia. Shi dai Messi yana fama ne da rauni a kwaurinsa na dama. Angel Di Maria mai shekaru 36 wanda ya yi ritaya daga bugawa qasarsa ta Argentina…
Read More
Yadda kocin D’Tigress ta yi zarra a Olympics

Yadda kocin D’Tigress ta yi zarra a Olympics

An zaɓi Rena Wakama a matsayin mafi ƙwarewar koci a gasar 2024 a birnin Paris bayan da ta jagoranci tawagar DTigress ta Nijeriya zuwa wasanni masu ban sha'awa a tarihin gasar ƙwallon kwando ta Olympics. Nijeriya ta nuna bajinta bayan da ta doke Australia a ranar buɗe gasar, wanda shi ne karon farko da tagawar ta samu nasara a wasan rukuni. Kwanaki kaɗan bayan haka, Nijeriya ta bai wa ƙasar Canada mamaki inda ta zama tawaga ta farko a nahiyar Afrika da ta samu nasara sau biyu a gasar, inda ta kuma yi tsayuwa tsayin daka wajen kare martabar ƙasarta.…
Read More
A shirye na ke in sauka daga shugabancin Olympics – Thomas Bach

A shirye na ke in sauka daga shugabancin Olympics – Thomas Bach

Shugaban Wasannin Olympics na ƙasa da ƙasa, Thomas Bach, ya ce zai sauka daga muƙaminsa idan wa'adinsa na biyu ya ƙare a shekarar 2025. Bajamushen ya ce, ba zai sake neman wani wa'adi a yarjejeniya ta Olympic ba. Bach ya bayyana hakan ne a wurin taron IOC na ranar ƙarshe na gasar Olympics ta Paris, yana mai cewa Olympics ta fi dacewa da canjin shugabanci lokaci-lokaci. “Akwai dama ga sabbin shugabanni. “Ni, a shekaru na, ba shugaba mafi dacewa ba ne. An zabi Bajamushen 1976 wanda ya lashe lambar zinare a cikin 2013 na tsawon shekaru takwas a matsayin magajin…
Read More
Ƙungiyar New England ta Amurka ta ɗauki ɗan wasan Nijeriya Yusuf Alhassan

Ƙungiyar New England ta Amurka ta ɗauki ɗan wasan Nijeriya Yusuf Alhassan

Ɗan wasan tsakiya na tawagar ƙwallo ƙafa ta Nijeriya, Yusuf Alhassan, ya koma ƙungiyar New England Revolution ta Amurka da taka leda. Ɗan wasan mai shekara 24 ya koma gasar Major League Soccer ta Amurka ne daga Royal Antwerp ta Belgium, inda ya shafe shekara uku a matsayin ɗan wasan tsakiyarta. Haifaffen jihar Kano, Yusuf ya saka hannu kan yarjejeniyar shekara uku da rabi zuwa 2027 tare da zaɓin tsawaita ta da shekara ɗaya. "Saboda ƙwarewarsa a wasannin ƙasa da ƙasa da kuma gasar zakarun Turai ta Champions League, ina sa ran Yusuf zai nuna kansa a matsayin babban ɗan…
Read More
Za mu ɗaukaka damben gargajiya na Nijeriya a duniya – Ministar Al’adu 

Za mu ɗaukaka damben gargajiya na Nijeriya a duniya – Ministar Al’adu 

Ministar Al'adu na Nijeriya, Barista Hannatu Musa Musawa ta ce haɗin gwiwa da ƙungiyar Dambe Warriors League (DWL) za ta bunƙasa wasannin gargajiya na Nijeriya da tare da bayyana shi a duniya. Ministar ta bayyana haka ne a lokacin da shugabannin ƙungiyar Dambe Warriors League suka kai mata ziyarar ban girma a Abuja ranar Alhamis. A cewar wata sanarwa da mai ba da shawara na musamman kan harkokin yaɗa labarai ga Ministar Al’adu da, Nneka Ikem Anibeze, ya fitar a ranar Juma’a, Musawa ta bayyana farin cikinta ga masu shirya gasar da ke da alhakin bunƙasa wasannin gargajiya na Dambe.…
Read More
Hada-hadar kasuwar ’yan wasan ƙwallon ƙafa

Hada-hadar kasuwar ’yan wasan ƙwallon ƙafa

West Ham na neman ɗaukar ɗan wasan bayan Chelsea da Ingila mai shekara 26, Treɓoh Chalobah, da kuma ɗan wasan bayan Jamus mai shekara 35, Mats Hummels, wanda kwangilarsa da Borussia Dortmund ta ƙare a bana. Crystal Palace na zawarcin ɗan wasan bayan Chelsea Chalobah, ta na kuma bibiyar ɗan wasan bayan Faransa mai shekara 24, wanda ke leda a Wolfsburg, Maxence Lacroix. Har yanzu Liverpool na da sha'awar ɗaukar ɗan wasan gaban Jamus da Hoffenheim, Maximilian Beier, amma ɗan wasan mai shekara 21 ya fi son komawa Borussia Dortmund. Ɗan wasan bayan Aston ɓilla mai shekara 31, Lucas Digne…
Read More
Na fuskanci ƙalubale zuwa na Chelsea – Caicedo

Na fuskanci ƙalubale zuwa na Chelsea – Caicedo

Moises Caicedo, ya ce kakarsa ta farko a Chelsea ta kasance "mai tsauri" kuma ya kasa samun kwarin gwiwa, saboda an saye shi kan farashin fam miliyan 115. Ɗan wasan tawagar Ecuador, mai shekara 22, ya koma Chelsea daga Brighton a watan Agustan bara kan fam miliyan 100, har da ƙarin tsarabe-tsarabe da ya kai fam miliyan 115. ƙungiyar Stamford Bridge ta ɗauki ɗan wasan a matakin mafi tsada a Birtaniya, bayan da Liverpool ta yi zawarcinsa. Ya ci ƙwallo daya ya bayar da huɗu aka zura a raga a wasa 48 a kakarsa ta farko a Chelsea, wadda ta…
Read More
Alvarez zai cigaba da buga wa Man City – Guardiola

Alvarez zai cigaba da buga wa Man City – Guardiola

Kocin Manchester City, Pep Guardiola, ya bayyana Julian Alvarez a matsayin "ɗan wasan mai zimma" yayin da yake amsa tambayoyi game da makomar ɗan wasan Argentina. An tambayi makomar Alvarez, wanda ake alakanta mai shekara 24 da cewar zai koma Atletico Madrid, bayan da City ta ci Chelsea 4-2 a filin wasa na Ohio. "Babu abin da zan ce. Alvarez zai ci gaba da taka mana leda idan ya kare hutu, bayan Copa America da Olympic da ya buga," in ji Guardiola. Alɓarez, wanda kwantiraginsa a City zai kare a ƙarshen kakar 2028, ya buga wa Argentina gasar Olympics a…
Read More
Tsohon shugaban CAF, Issa Hayatou, ya rasu

Tsohon shugaban CAF, Issa Hayatou, ya rasu

Tsohon shugan hukumar ƙwallon kafa ta Afirka CAF Issa Hayatou ya rasu. Hayatou, wanda ɗan ƙasar Kamaru ne, ya rasu saura kwana ɗaya ya cika shekara 78 a duniya a birnin Paris. Hayatou ya kasance Shugaban ƙungiyar da yafi kowa jimawa kan karagar mulki. Ya hau kujerar a shekarar 1988 har zuwa 2017. A lokacin shi, ƙwallon ƙafa a Afirka ta samu cigaba sosai, ɗaya daga cikin abun jajircewar da yayi shine kawo gasar kofin duniya Afirka karo na farko. Ya taka rawa wajen ganin Afirka ta samu ƙarin gurbi a gasar cin kofin duniya. Hayatou ya taɓa riƙe shugabancin…
Read More