20
Jul
Ɗan wasan gaba na gefe na Leeds Crysencio Summerɓille, mai shekara 22, ya tattauna da Chelsea, to amma kuma ƙungiyar Rennes ta Faransa, ita ma ta yi magana da ɗan Holland ɗin. Huddersfield Town na tattaunawa domin sayen ɗan wasan tsakiya na Wolɓes Joe Hodge, mai shekara 21, bayan da ɗan wasan na tawagar Jamhuriyar Ireland ta 'yan ƙasa da shekara 21 ya shafe kakar da ta wuce a zaman aro a Ƙueens Park Rangers. Barcelona ta gabatar da buƙatarta ga ɗan wasan gaba na gefe na Athletic Bilbao Nico Williams, mai shekara 22, a ƙoƙarin cimma yarjejeniya ta baki…
