Wasanni

Ahmed Musa ya shirya komawa Kano Pillars – Rahoto

Ahmed Musa ya shirya komawa Kano Pillars – Rahoto

Daga WAKILINMU Rahotanni sun tabbatar cewa fitaccen ɗan wasan ƙwallon ƙafar nan kuma kyaftin a Super Eagles, wato Ahmed Musa, na shirin sake komawa ƙungiyar Kano Pillars don yin aiki na taƙaitaccen lokaci. Musa, ɗan shekara 28, ya kasance ba ya buga ma wata kulob wasa tun daga Otoban 2020, bayan kammala harƙallarsa da ƙungiyar Al Nassr ta ƙasar Saudiyya, bayan kuma ya kasa samu ƙulla wata harka a Turai. Bayanai sun nuna ana sa ran tsohon ɗan wasan Leicester City ɗin zai yi aiki na ɗan lokaci tare da Kano Pillars. Kanawa na matuƙar martaba ɗan wasan tun bayan…
Read More
Wasanni: Dare ya gargaɗi ‘yan wasa su guji yin amfani da muggan ƙwayoyi

Wasanni: Dare ya gargaɗi ‘yan wasa su guji yin amfani da muggan ƙwayoyi

Daga BASHIR ISAH Ministan Wasannin Motsa Jiki, Chief Sunday Dare, ya yi kira ga 'yan wasa da su guji yin amfani da ƙwayoyin ƙara kuzari da duk wani nau'i na fitina. Ministan ya yi wannan kira ne yayin rangadin da ya je don duba wuraren wasanni na bikin wasannin motsa jiki na ƙasa (NSF) karo na 20 da ke gudana a Benin, babban birnin jihar Edo. Dare wanda shi ne ya wakilci Mataimakin Shugaban Ƙasa, Yemi Osinbajo a wajen taron buɗe bikin, ya ce bikin zai taimaka wajen gano 'yan ƙasa masu fasaha a sha'anin wasannin motsa jiki. Binciken Manhaja…
Read More
Koriya ta Arewa ta janye daga gasar Olympics saboda tsoron cutar korona

Koriya ta Arewa ta janye daga gasar Olympics saboda tsoron cutar korona

Daga WAKILINMU Koriya ta Arewa ta bada sanarwar ba za ta halarci gasar Olympics da aka shirya gudanarwa a Ƙasar Tokyo ba a cikin wannan shekara saboda dalili na neman kare 'yan wasanta daga kamuwa da cutar korona. Koriya ta Arewa ta ce na musamman ta ɗauki wannan mataki domin kare 'yan wasanta gudun kada su harbu da cutar korona. Wannan mataki da ƙasar ta ɗauka ya katse wa Koriya ta Kudu damar da ta hango na yin amfani da gasar wajen tattaunawa da takwararta Koriya ta Arewa game da abin da ya shafi kan iyaka. A 2018 ƙasashen biyu…
Read More
Ondo: ‘Yanwasan Sunshine Stars sun yi zanga-zanga saboda rashin biyan albashi

Ondo: ‘Yanwasan Sunshine Stars sun yi zanga-zanga saboda rashin biyan albashi

Daga UMAR M. GOMBE 'Yanwasa da jami'an Ƙungiyar Ƙwallon Kafa ta Sunshine Stars a Jihar Ondo, sun gudanar da zanga-zanga domin nuna rashin jin daɗinsu kan abin da suka kira da rashin kulawa daga ɓangaren Gwamnatin Jihar. Zanga-zangar wadda aka gudanar a birnin Akure ta yi sanadiyar haifar da tsaiko ga harkokin kasuwanci a yankin. Masu zanga-zangar sun yi tattaki ne daga babban filin wasannin motsa jiki zuwa fadar gwamnatin jihar ɗauke da kwalaye masu dauke da saƙonni daban-daban don nuna damuwarsu. Waɗanda lamarin ya shafa sun ce ba su samu albashinsu ba na tsawon wata shida haɗa da sauran…
Read More
AFCON 2022: Super Eagles ta tsallake siraɗi

AFCON 2022: Super Eagles ta tsallake siraɗi

Ƙungiyar Ƙwallon Ƙafa ta Nijeriya, Super Eagles, ta samu nasarar shiga gasar Cin Ƙofin Ƙasashen Afirka (AFCON) wadda aka shirya gudanarwa a ƙasar Kamaru a 2022. Nijeriya ta samu wannan nasarar ce sakamakon kunnen doki na rashin jefa ƙwallo a raga da Lesotho da Saliyo suka yi a rana ta biyar na buga wasan cancantar shiga gasar.
Read More
‘Yan wasa 8000 ne za su fafata a bikin wansannin motsa jiki na Edo – Minista

‘Yan wasa 8000 ne za su fafata a bikin wansannin motsa jiki na Edo – Minista

Daga UMAR M. GOMBE Gwamnatin Tarayya ta bada tabbaccin za a gudanar da bikin wasannin motsa jiki da aka shirya gudanarwa a jihar Edo kamar yadda aka tsara. Ministan Harkokin Matasa da Wasannin Motsa Jiki, Chief Sunday Dare ne ya bada wannan tabbaci a garin Benin, Juma'ar da ta gabata. A cewar Dare, bikin wanda ake sa ran ya ƙunshi 'yan wasa 8000, zai gudana ne daga ranar 2 zuwa 4 ga Afrilun 2021. Da yake jawabi bayan kammala zagayen duba kayayyakin wasa da kuma ganawa da gwamnan jihar, Godwin Obaseki, Ministan ya ce, "za a buɗe sansanin 'yan wasa…
Read More
Kenya: An yanke wa ‘yar wasan tsere hukuncin shekara guda saboda amfani da maganin ƙara kuzari

Kenya: An yanke wa ‘yar wasan tsere hukuncin shekara guda saboda amfani da maganin ƙara kuzari

Daga FATUHU MUSTAPHA Wata kotun ƙasar Kenya ta yanke wa ‘yar wasan tseren asar, Florence Jepkosgei, hukuncin yi wa al’umma hidima na tsawon shekara guda bayan da ta kama ta da laifin gabatar da takardun bogi na ƙoƙarin kare kanta daga laifin yin amfani da ƙwayoyin ƙara kuzari, in ji Ƙungiyar Yaƙi da Amfani da Abubuwan Ƙara Kuazara ga ‘Yanwasa ta Kenya (ADAK). Da wannan, Florence ta zama ‘yar tseren Kenya ta farko da aka taɓa yanke wa hukuncin manyan laifuka a kotu. An shafe shekaru ana gudanar da bincike kan wannan batu kafin a kai ga yanke hukunci a…
Read More
’Yan wasan damben boksin da su ka fi samun kuxi a duniya

’Yan wasan damben boksin da su ka fi samun kuxi a duniya

Daga UMAR M. GOMBE Ɗaya daga cikin manyan wasannin da suka fi shahara a duniya shi ne, wasan damben zamani da ake kira a turance da Boxing. Kusan a iya cewa wannan wasa na cikin wasanni mafiya daɗewa a duniya, domin kuwa wasan dambe wasa ne da kusan ba wata al’umma da bata yi. Masana sun gano cewa, akwai shaidu na tarihi da suka nuna shekaru 3000 kafin bayyanar Annabi Isa ana wannan wasa a tsohuwar Daular Misra. Amma wasan ya fara samun tagomashi ne a ƙarni na 7 tunda aka fara yin sa a wasan Olympic. Sai dai duk…
Read More
Gasar ƙwallon ƙafa: Ekiti ta shirya karɓar baƙi

Gasar ƙwallon ƙafa: Ekiti ta shirya karɓar baƙi

Daga BASHIR ISAH A halin da ake ciki jihar Ekiti ta ce ta shirya tsab domin karɓar baƙuncin ƙungiyoyin ƙwallon ƙafa su 16 daga jihar Kwara da na sauran jihohi daga shiyyar Kudu maso-yamma sakamakon gasar ƙwallon ƙafa ta ƙasa da aka shirya gudanarwa a jihar. A zantawarsu da manema labarai, Shugaban Ƙungiyar Ƙwallon Ƙafa na Jihar, Ekiti Bayo Olanlege, ya bayyana farin cikinsa tare da bada tabbacin cewa jihar ta shirya karɓar baƙi albarkacin gasar. Olanlege ya yi amfani da wannan dama wajen yi wa baƙinsu albishir da cewa lallai za su ji daɗin gwargwadon zaman da za su…
Read More