Daga CMG HAUSA
Sashen gidan rediyo da talabijin na Sin, wato CMG dake nahiyar Amurka ta Arewa ya fitar da shirin “shawarar daukar matakin neman bunkasuwa na 2022” a shafin yanar gizo, inda aka mai da hankali kan sauyin yanayi da ci gaba mai dorewa. Manyan mutane da dama da suka hada da babban sakataren MDD da shugaban asusun IMF da shugabannin wasu kasashe uku, sun yi kira ga kasa da kasa ta dandamali da yaw ana CMG, sun gabatar da shawarwarinsu na neman ci gaba mai dorewa.
Bana ce shekara ta uku da sashen CMG dake nahiyar Amurka ta Arewa ya gabatar da “shawarar daukar matakin neman bunkasuwa”. Sakamakon haka, babban sakataren MDD António Guterres ya ce wannan shawara ita ce “babban kokarin da aka yi wajen inganta cimma makasudin neman ci gaba mai dorewa na MDD”.
Tun bayan sashen CMG dake nahiyar Amurka ta Arewa ya fitar da shawarar, aikin da CMG ya yi a kowace shekara ya zama muhimmin dandali, inda muhimman ’yan siyasa na kasashen duniya da hukumomin zamantakewa da masana suke more nasarori da darussan da aka samu wajen neman ci gaba mai dorewa. Rahotanni masu alaka da aka bayar, sun isa mutane kimanin miliyan 400.
Mai fassara: Safiyah Ma