Da Ɗumi-ɗumi: Abba Kabir ya karɓi shaidar lashe zaɓen Gwamnan Kano

Daga RABI’U SANUSI a Kano

Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) reshen Jihar Kano, ta miƙa wa zaɓaɓɓen gwamnan jihar ƙarƙashin jam’iyyar NNPP shaidar lashe zaɓen gwamnan jihar.

Abba Kabir Yusuf da mataimakinsa, Kwamared Abdulsalam Gwarzo sun karbi satifiket ɗin ne ranar Laraba a babban ofishin INEC da ke Kano.

Cikin waɗanda suka halarci taron miƙa shaidar, akwai Shugaban hukumar zaben na Kano, Ambasada Zango Abdu, Kwamishinan ‘Yan Sandan Jihar Kano, CP Mamman Dauda da dai sauran jiga-jigan jam’iyyar NNPP na ciki da wajen jihar.