Da ɗumi-ɗumi: APC ta tsige Buni ta maye gurbinsa da Bello

A halin da ake ciki Gwamna Sani Bello na jihar Neja yanzu shi ne ke riƙe da akalar jam’iyyar APC mai mulki.

Wannan ya faru ne biyo bayan tsige Gwamna Mai Mala Buni da jam’iyyar ta yi a matsayin shugabanta na riƙo.

Yanzu haka Gwamna Bello na can na jagorantar taron kwamitin riƙo na APC tare da ciyamomin jam’iyyar na jihohi kan shirye-shiryen babbaron taron da za su gudanar ya zuwa ƙarshen wannan wata.

Taron nasu na gudana ne a babbar sakatariyar APC da ke Abuja.

Cikakken rahoto na nan tafe.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *