Daga SANUSI MUHAMMAD a Gusau
Rahotanni sun nuna cewa wasu mutane da ake kyautata zaton ‘yan bindiga ne sun harbe dan takarar gwamna a ƙarƙashin jam’iyyar APC a zaɓen 2019 har lahira a jihar Zamfara akan hanyar Abuja zuwa Kaduna.
Rahoton ya ce, lamarin ya faru ne a ƙauyen Rijana da yammacin jiya Lahadi.
Tuni jami’an tsaro suka kai gawar marigayi Sagir Hamidu Gusau asibitin garin Kaduna inda ake sa ran a miƙa gawar ga iyalan mamaci a yau Litinin da safe domin yi masa jana’iza kamar yadda addinin Musulunci ya tanada.