Da Ɗumi-ɗumi: ‘Yan bindiga sun kashe mahaifin shugaban ƙaramar hukuma a Kano

Daga IBRAHIM HAMISU, a Kano

Wasu ‘yan bindiga da ba a tantance su ba sun kashe Hakimin Maigari a Ƙaramar Hukumar Rimin Gado a Jihar Kano, Alhaji Ɗahiru Abba.

Sabon babban sakataren shari’a na Jihar Kano, Alhaji Sanusi Abbas, wanda kuma ɗan gidan marigayin ne ya tabbatar da faruwar lamarin, kamar yadda majiyarmu ta Justice Watch ta ruwaito.

A cewarsa, marigayin shi ne Hakimin ƙauyen Maigari, kuma uba ga Shugaban Ƙaramar Hukumar Rimin Gado na yanzu, Barista Munir Dahiru Maigari.

“Marigayi Maigari ya rasu ne bayan da wasu ‘yan bindiga da ba a san ko su wane ne ba suka kai wa gidansa hari da sanyin safiyar Lahadi, inda suka yi masa raunuka daban-daban daga bisani suka harbe shi har lahira,” in ji shi.

Ya ƙara da cewa, za a yi jana’izar ne da safiyar Lahadi a gidansa a ƙauyen Maigari da ke cikin Ƙaramar Hukumar Rimin Gado, jihar Kano.