DSS ta yi gargaɗi kan take-taken neman tada rikici a ƙasa

Daga AISHA ASAS

Hukumar Tsaro ta DSS, ta yi gargaɗi kan take-taken da wasu mutane da kuma ƙungiyoyi ke yi na neman haddasa rikicin addini da na ƙabilanci a wasu sassan ƙasa.

Jami’in Hulɗa da Jama’a na Ƙasa na hukumar, Dr Peter Afunanya, shi ne ya yi wannan gargaɗi a wani bayani da ya yi a Abuja, a ranar Laraba.

Ko a ranar 11 ga Janairun da ya gabata, sai da hukumar ta yi makamancin wannan gargaɗi inda ta ce, akwai wasu da ke mummunan tanadi don tayar da rikicin addini a ƙasa.

A cewar DSS, wuraren da ake hari don kunna wutar rikicin sun haɗa da; Sakkwato da Legas da Filato da Rivers da Oyo da Kaduna da sauran wurare a yankin Kudu maso-gabas.

Ta ƙara da cewa, manufar ɓatagarin ita ce tayar da rikicin addini sannan su yi amfani da ‘yan barandansu wajen kai hare-hare a wuraren ibada da shugabannin addini haɗa da wasu fitattun mutane a cikin al’umma da dai sauransu.

Afunanya ya ce, masu wannan mummunan tanadi suna nan sun bada himma wajen furta kalaman da ka iya harzuƙa jama’a da kuma ingiza mutane kan junansu don kawai su samu damar kunna wutar rikicin addini da na ƙabilanci.

“Hukumar DSS za ta yi aiki tare da takwarorinta da sauran hukumomin da suka dace, wajen ɗaukar matakan da suka dace don ci gaba da kare rayuka da dukiyoyin ‘yan ƙasa”, inji Afunanya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *