Faɗuwar Goro a Fagge: Mai ɗaki shi ya san wurin da yake masa yoyo

Manhaja logo

Daga KABIRU YUSUF FAGGE (ANKA)

Kamar yadda Hausawa kan ce: “Mai ɗaki shi ya san inda yake masa yoyo,” al’ummar Fagge suna yin zaɓe ne bisa cancanta, sannan idan ka yi abin yabawa, za su yaba maka. Idan ka kauce, su kawar da kai.

Shi ɗan majalisarmu na tarayya da muka zaɓa, da wuyansa ya yi kauri, sai yake ganin manya da matasa da yaran ƙaramar hukumar Fagge ba su ishe shi kallo ba.

Da munin ya yi yawa ma, lokacin zaɓen 2023 ya tunkaro sai ya ɗauko yuyar ‘yan daba ya shigo kamfen cikin unguwar cikin wani yanayi na “shege-ka-fasa”. Aka zo zaɓen cike gurbi, mutumin nan yana matsayi na uku, amma sai da ya sake tafka kuskuren bai wa ‘yan daba damar cin karensu ba babbaka, ya nemi su hargitsa waɗanda yake gani ba za su zaɓe shi ba; wannan kuma shi ne ƙarin gagarumin kuskuren da ya sake tafkawa, don wallahi iya sani da ‘yan Fagge sun tsani siyasar daba, ba sa jurar rainin wayo da tilastawa.

Don haka, kaso 95% na mutanen ƙaramar hukumar Fagge sun yi murna da faɗuwar Goro. Wannan shi ne faɗuwar baƙar tasar, domin mutanen Fagge ba za su manta ƙarfa-ƙarfar ba, kamar yadda ba su manta dalilin da ya sa suka zaɓe ka sau uku ba.

A ƙarshe wani zai yi min maganar gonar ofa da ba da jari da aka ce musu yana yi. E, amma ba al’ummar Fagge ake zuwa wa da irin wannan rainin wayon ba, don ba za ka rinƙa bai wa ‘yan gaban-goshinka ofa kana hana waɗanda suka cancanta ba. Kana ’empowerment’ ɗin mutanenka kana hana waɗanda suka cancanta, alhalin haƙƙinsu ne.

Sannan ga ilimi ga wayewa, sun san yadda tsarin ofar take, akwai ta gaske akwai ta rainin wayo.

Muna fatan wannan ya zama darasi gare ka da sauran ‘yan siyasa masu sauya hali.

Kamar yadda muke yi wa duk wanda ya lashe zaɓe fatan alheri, muna yi wa Barrister MB Shehu fatan yin nasarori a yayin mulkinsa, ya kauce halayya irin waɗannan, amin.

Kabiru Yusuf Fagge, ɗan ƙasa ne mai bayyana ra’ayi. Ya rubuto ne daga Kano.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *