Ƙungiyar Masu Shiga-tskanin Harkokin Ƙwallon Kafa ta Kasa (FIAN), ta nuna damuwarta kan yadda masu ruwa da tsaki kan harkokin ƙwallon ƙafa ba su ɗaukar lamarin ‘yan ƙwallon da muhimmanci wajen biyan albashinsu da alawus-alawus da makamantansu yadda ya dace.
Shugaban FIAN na ƙasa, Ayodele Thomas, ya nuna damuwarsa kan yadda masu ƙungiyoyin ƙwallon ƙafa suke nuna halin ko-in-kula wajen kula da sha’anin ‘yan wasansu yadda ya kamata.
Da yake zantawa da manema labarai, Thomas ya ce abin takaici ne yadda masu kulob-kulob kan gaza wajen lura da ‘yan ƙwallonsu bilhaƙki.
Ya ce kamata ya yi kafin ƙungiya ta ɗauki wani ɗanwasa ta tuntuɓi masu shiga tsakani don samun daidaito yadda ya kamata, amma haka ba ya faruwa wanda hakan kuwa abin kunya ne.
Ya ci gaba da cewa, irin haka ba daidai ba ne saboda ya saɓa wa tsarin harkar ƙwallo, sannan faruwan hakan kan hana ɓangarorin ƙungiyoyi da ‘yanwasa da ma hukumar ƙwallon ƙafa ta ƙasa cigaba.
A ƙarshe, Thomas ya bayyana aniyar da suke da ita ta neman haɗa kai da ƙungiyar ‘yan wasa da duka waɗanda suka dace domin yin aiki tare wajen inganta sha’anin ‘yanwasa da ma bunƙasa harkokin ƙwallon ƙafa a faɗin ƙasa baki ɗaya.