Gasar ƙwallon ƙafa: Ekiti ta shirya karɓar baƙi

Daga BASHIR ISAH

A halin da ake ciki jihar Ekiti ta ce ta shirya tsab domin karɓar baƙuncin ƙungiyoyin ƙwallon ƙafa su 16 daga jihar Kwara da na sauran jihohi daga shiyyar Kudu maso-yamma sakamakon gasar ƙwallon ƙafa ta ƙasa da aka shirya gudanarwa a jihar.

A zantawarsu da manema labarai, Shugaban Ƙungiyar Ƙwallon Ƙafa na Jihar, Ekiti Bayo Olanlege, ya bayyana farin cikinsa tare da bada tabbacin cewa jihar ta shirya karɓar baƙi albarkacin gasar.

Olanlege ya yi amfani da wannan dama wajen yi wa baƙinsu albishir da cewa lallai za su ji daɗin gwargwadon zaman da za su yi a jihar.

Haka nan, ya ce duka wurare da kayayyakin wasan da ake buƙata don gudanar da gasar an tanade su kuma a kimtse suke.

Daga nan jami’in ya yaba wa gwamnan jihar, Dr. John Kayode Fayemi dangane da irin ƙoƙarin da yake yi wa harkar wasannin motsa jiki a jihar domin ganin fannin ya bunƙasa yadda ya kamata.

Yayin da Olanlege ya ce gasar za ta taimaka wa ‘yan kasuwa da kuma tattalin arzikin jihar saboda tarin baƙi da za su shigowa daga waje, haka ma ya ce ba za a yi sake ba wajen kula da dukkan dokokin yaƙi da cutar korona da aka shimfiɗa.