Gumi da Obasanjo sun taimaka wajen kuɓutar da daliban Kaduna 27 da aka yi garkuwa da su

Daga WAKILINMU

Bayanai daga jihar Kaduna, sun nuna an sako ɗaliban College of Forestry Mechanisation da ke Afaka a jihar su 27 da aka yi garkuwa da su. Ɗaya daga cikin waɗanda suka karɓi ɗaliban ne ya labarta wa jaridar Daily Trust batun.

Majiyar Daily Trust ta ce kwamitin sulhu na Sheikh Ahmed Gumi shi ne ya shige gaba wajen kuɓutar da ɗaliban, tare da taimakon Tsohon Shugaban Ƙasa, Olusegun Obasanjo.

Ɗaliban na daga cikin ɗalibai 37 da aka sace a jihar kusan watanni biyu da suka gabata. Inda bayan biyan kuɗin fansa da iyayen ɗaliban suka yi, sai ‘yan fashin suka saki ɗalibai 10 daga ciki.

Da farko ɓarayin sun buƙaci gwamnatin jihar Kaduna ta biya su kuɗi har Naira milyan N500 kafin su amince su saki ɗaliban, amma sai Gwamna Nasir El-Rufai ya ce atabau babu wata fansa da za a biya, tare da cewa kisa ita ce daidai da ‘yan fashi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *