Gwamna Bello ya naɗa sabon shugaban ma’aikata

Daga FATUHU MUSTAPHA

Gwamnan jihar Kogi, Alhaji Yahaya Bello, ya naɗa Mrs. Hannah Odiyo a matsayin sabuwar Shugaban Ma’aikata na Gwamnatin Jihar.

Sakataren Gwamnatin Jihar, Dr. Folashade Arike Ayoade ne ya sanar da hakan a wata sanarwa da ya fitar a ranar Alhamis.

Kafin naɗin nata, Mrs. Odiyouta ta kasance riƙe da matsayin sakatariyar Ma’aikatar Harkokin Noma na Jihar Kogi.

Gwamna Bello ya yi yabo na musamman ga shugabar ma’aikata mai barin gado, Deborah Ogunmola dangane da irin gudunmawar da ta bayar ga cigaban sha’anin aikin gwamanti a jihar.

Kana ya taya sabuwar shugabar murnar samun sabon muƙami tare da yi mata fatan alheri.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *