Gwamnan Kano ya aike wa majalisa sunayen mutanen da zai naɗa kwamishinoni

Daga IBRAHIM HAMISU a KANO

Gwamnan kano Dr Abdullahi Umar Ganduje ya miƙa wa majalisar Dokokin Jihar Kano sunayen mutane 8 da yake so a ba su matsayin Kwamishinoni na jihar Kano,

Gwamnan Ganduje ya aikewa shugaban majalisar dokokin Kano Injiniya Hamisu Ibrahim Chidari buƙatar amince masa ya naɗa sabbabbin kwamishinoni ta cikin wata wasiƙa da aike masa,

Mutanen da gwamnan ya tura sunayen nasu sun haɗa da:

 1. Ibrahim Dan Azumi Gwarzo
 2. Garba Yusuf Abubakar
  3 .Adamu Abdu Fanda
  4 .Yau Abdullahi Yan Shana
  5 .Sale kausari
  6 .Yusuf Jibrin Ruruwai
  7 .Abdulhamid Abdullahi Liman
  8 .Lamin Sani Zawiyya

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *