Gwamnatin Tarayya ta musanta nuna ƙabilanci wajen kwaso ’yan Nijeriya daga Sudan

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Gwamnatin Tarayya ta yi watsi da zarginta da nuna ɓangaranci ko kuma ƙabilanci wurin kwaso ‘yan Nijeriyar da ke Sudan.

A wani bidiyo da ya karaɗe shafukan sada zumunta, an ga wani mutum yana magana da harshen Igbo inda ya bayyana cewa an ƙi kwaso wasu daga cikinsu saboda ƙabilanci.

Sai dai a wata sanarwa da Ma’aikatar Harkokin Wajen Nijeriya ta fitar, ta bayyana cewa babu ƙamshin gaskiya a iƙirarin da mutum ya yi.

“Ma’aikatar ta yi bincike kan zarge-zargen da ya yi kuma tana tabbatar wa ‘yan Nijeriya cewa babu gaskiya a zarge-zargen da ya yi.

“Ofishin Jakadancin Nijeriya a Khartoum ya tabbatar da cewa ‘yan ƙabilar Igbo na daga cikin rukunin farko na ‘yan ƙasar 637 da aka kai iyakar Aswa a Masar inda suke jira a mayar da su Nijeriya,” kamar yadda sanarwar Ma’aikatar Harkokin Wajen Nijeriyar ta bayyana.

Hasali ma ma’aikatar ta wallafa hotunan wasu daga cikin ’yan ƙabilar Igbo da ke zaune a Sudan da ta kwaso.

Ma’aikatar ta ƙara da cewa kafin a soma kwasar ‘yan ƙasar zuwa kan iyaka, sai da aka samu rashin jituwa tsakanin ɗaliban Nijeriya da kuma ‘yan Nijeriyar da ke zama a Sudan sakamakon ƙarancin motoci.

Amma ma’aikatar ta ce duk da haka an samar da motoci domin kwasar duk wani ɗan Nijeriya da ke zaune a Sudan kuma yake so ya bar ƙasar.

’Yan Nijeriya da dama ne gwamnatin ƙasar ta kwaso daga Sudan sakamakon rikicin da ake yi a ƙasar, sai dai an samu tsaiko wurin mayar da su Nijeriyar sakamakon wasu dalilai.

Daga ciki kuwa har da jinkirin da aka samu wurin kwaso su da kuma maƙalewar da ’yan ƙasar suka yi kan iyakar Masar da Sudan sakamakon kin buɗe iyakar da Masar ƙin ba ta yi ba ga ’yan Nijeriya.

Rahotanni sun bayyana cewa an kwaso rukunin farko na ’yan Nijeriya da suke ƙoƙarin tserewa rikicin da ya varke a Sudan.

Bayanai sun ce an kwaso ’yan Nijeriyar ne daga filin jirgin saman Aswan da ke ƙasar Masar.

Tun da farko dai an sa ran tasowar ’yan Nijeriyar da misalin kƙarfe 1 na rana a jirgin Sojin Saman Ƙasar na NAF C130 da wani jirgin Air Peace da fasinjoji 274, amma hakan bai samu ba.

Lamarin na zuwa ne bayan da hukumomin Masar suka sharɗanta cewa dole ne duk waɗanda za a kwashe su bar ƙasarsu nan take.

Majiyoyi sun shaida wa Blueprint cewa, an ba wa mutanen damar shiga filin jirgin saman Masar ne tsakanin daren Talata zuwa safiyar Laraba.

A bayan nan ne dai Gwamnatin Masar ta ce ta yarda a kwashe ’yan Nijeriya da ke tsere wa faɗan da ake yi a Sudan ta kasarta.

Shugabar Hukumar Kula da ’Yan Nijeriya Mazauna Ketare NiDCOM, Abike Dabiri-Erewa ce ta tabbatar da wannan lamari a ranar Litinin.

A cewarta, Gwamnatin Masar ta bayar da lamunin ne bayan da Shugaba Muhammadu Buhari ya nemi alfarma daga wajen takwaransa na Masar ɗin, Shugaba Abdel Fattah El-Sisi.