Gyaran Dokar Zaɓe: Sanatoci sun ƙi amincewa da buƙatar Buhari

Daga BASHIR ISAH

A zamanta na ranar Laraba, Majalisar Dattawa ta ƙi amincewa da buƙatar Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ta neman yi wa Sashe na 84(12) na Dokar Zaɓe kwaskwarima, sashen dokar da ya hana masu riƙe da muƙaman siyasa tsyawa takarar fidda gwani ba tare da sun ajiye muƙaman nasu ba.

Bayan da Jagoran Majalisar, Yahaya Abdullahi (APC Kebbi ta Arewa) ya jagoranci muhawarar nazarin dokar a karo na biyu, a nan aka samu da yawa daga cikin sanatocin suka ƙi amincewa da buƙatar bayan da Shugaban Majalisar, Ahmad Lawan ya gabatar musu da batun don yin ƙuri’a.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *