Daga ABBA ABUBAKAR YAKUBU
Musa Sani Aliyu wanda aka fi sani da Musa Khan, ma’aikaci ne a gidan rediyon Jalla da ke birnin Kano. Wata rana da daddare misalin ƙarfe tara a kan hanyarsa ta komawa gida bayan ya tashi daga wajen aikinsa a daidai kan titin Club Road kusa da ofishin Kwastom yayin da yake tafiya wasu vata gari a kan babur suka sha gabansa yayin da suka nemi ya bada wayar da ke jikinsa, kafin ya sa hannu ya zaro wayar daga aljihunsa, sai ɗaya daga cikin su ya fitar da wata wuƙa da ke jikinsa da aka yi wa ƙira ta musamman, ya sare shi a hannu. Zafin wannan saran ya sa Musa ya yi kuwwa domin neman taimako, ganin yadda jama’a suka fara nufowa wajen ya sa nan da nan ɓarayin suka hau babur ɗinsu suka gudu. Ganin yadda jini ke zuba daga jikinsa inda suka sare shi sai aka garzaya da shi asibiti, domin ceto rayuwarsa.
Musa Khan ɗaya ne daga cikin ɗaruruwan mutanen da suka tsallake rijiya da baya, yayin harin da ‘yan daba masu ƙwacen waya suka kai musu a lunguna da anguwanni daban daban na cikin birnin Kano, da sauran manyan biranen arewacin ƙasar nan.
Rahotannin da ke fitowa daga jihohi daban daban, irin su Kano, Kaduna, Katsina, Filato, Bauchi, Gombe, Adamawa da sauran birane da dama na bayyana cewa, ana samun munanan hare hare daga miyagun matasa waɗanda shekarun su ba su wuce 14 zuwa 25 ba, da ke ɗauke da muggan makamai kuma suke far wa mutanen da ba su ji ba ba su gani ba, a kan tituna, da lunguna, har da cikin ababen hawa da gidaje, suna ƙwace musu wayoyinsu na hannu da wasu abubuwa da suka mallaka, wani lokaci ma an ce har ruwa mai guba na asid suke watsawa mutane, don jikkata su da yi musu lahani, har ma da kisan gilla.
A wasu lokutan waxannan matasa kan yi amfani da wuraren taruka kamar na siyasa, buki ko kuma idan an samu cinkoson ababen hawa a kan tituna sai su yi amfani da makami kamar wuƙa, adda, musilla, ƙaho, da wasu makamai masu ban tsoro, wajen yi wa mutane ƙwace. Yayin da suke wa mutane barazana a kan idan har basu bayar da abin da suke buƙata ba sai sun yi musu rauni ko ma su hallaka su baki ɗaya.
Kuma abin takaici a yayin da suke wannan mummunar ɗabi’ar ba sa ƙyale yara, da mata, ballantana dattijai masu rauni. Wasu daga cikin mazauna birnin Kano sun ce irin wannan ƙwace na waya ba wai na kan hanya kawai ake yi wa ba, a kan je har gida a yi sallama da mutum sannan a nemi ya bayar da wayarsa idan bai bayar ba sai a sa masa makami, a jikkata shi ko a kashe.
Wasu rahotanni na bayyana cewa a kowacce rana aƙalla mutane 15 ne suke gamuwa da ibtila’in sara da wuƙa ko wani makami ta dalilin ƙwacen waya a Jihar Kano. Yayin da a wata guda ake samun mutanen da tsautsayi ke faɗawa kansu ta dalilin qwacen waya da yawan su ya kai 450.
A daidai lokacin da nake wannan rubutu masu ƙwacen waya sun kashe mutane biyu cikin mako guda a Jos, ban da waɗanda ake jikkatawa kusan a kowacce rana. Abin da yake ƙara ɗaga hankalin masu faɗa a ji, da ke tattaunawa kan hanyoyin da za a bi a shawo kan wannan matsala da ke neman gagarar jami’an tsaro da ‘yan banga, duk kuwa da ƙoƙarin da suke yi ba dare ba rana, don kama masu aikata irin wannan ɗanyen aikin da gurfanar da su gaban ƙuliya.
Malam Nura Alhassan shi ne shugaban wata ƙungiyar matasa ta Jos Peace Vanguard, wacce ke taimakawa wajen wayar da kan matasa masu harkar daba da shaye-shaye, da canja musu tunanin su daga mummunar hanyar da suke kai, don su zama mutanen kirki kuma ‘yan ƙasa nagari. A wata ganawa da muka yi da shi ya bayyana min cewa, wannan matsala ta ƙwacen waya da ke daɗa ta’azzara na ƙara ɗaga musu hankali sosai, musamman ganin a baya an samu sauƙin matsalar sakamakon ƙoƙarin da suka yi na haɗa kan ƙungiyoyin matasa ‘yan daba masu gaba da juna tare da haɗin gwiwar jami’an tsaro, inda aka sasanta su tare da qulla yarjejeniyar daina rikici a tsakanin su, wanda sau da dama ke kaiwa ga kashe-kashe da sare saren juna. Amma tun farkon wannan shekarar ta 2023, harkar faɗan daba da ƙwacen waya ta sake kunno kai, musamman bayan dawowar harkokin siyasa.
Malam Nura ya ce, duk da yake jami’an tsaro na nasu ƙoƙarin amma ba za a naxe hannu a sa musu ido ba, dole ne za su sake yunƙurawa su ga sun gayyato tubabbun ‘yan daba da a baya suka yi ta fafutukar ceto su daga wannan mummunar hanya, domin amfani da su wajen zaƙulo kangararrun yaran da aka sani suna wannan abin da nufin zama da su don a daƙile cigaba da wannan mummunar halayya.
Ya ɗora alhakin dawowar harkokin ‘yan daba da amfani da makamai da yara matasa ke yi kan wasu baragurbin ‘yan siyasa da ke sanya matasan cikin gurɓatacciyar rayuwa ta shaye-shaye da kai hari kan abokan adawa, a duk lokacin da kuɗaɗen da suka saba bai wa yaran ya qare ko suka dakatar da ba su, shi ne suke komawa fashi da makami, da ƙwacen wayoyi don su samu abin sayen kayan maye.
A Jihar Kano ma inda nan ne aka fi samun wannan matsala a Arewa, ƙungiyoyi da jami’an tsaro na nan na fama da yaqi da waɗannan ‘yan daba da kusan a kowacce rana sai an samu rahoton ƙwacen waya da saran makami daga ɓangarori daban-daban na cikin birnin Kano. Abin da ya sa ma har rundunar ‘yan sandan jihar ta buɗe sashi na musamman mai yaƙi da wannan halayya da aka sa wa suna Anti-Daba Squad mai laƙabi da Rundunar Kan Ka Ce Kwabo, masu aikin kai ɗaukin gaggawa domin daƙile duk wata fitina da ke da nasaba da harkar ‘yan daba da ƙwacen waya. Kuma kamar yadda Kakakin rundunar ‘yan sanda ta Jihar Kano SP Abdullahi Haruna Kiyawa yake faɗa, jami’an tsaro na iyaka nasu ƙoƙarin amma idan dambu ya yi yawa ba ya jin mai, tilas sai jama’a sun sa hannu sun tallafawa gwamnati, domin kare rayukan su da dukiyoyinsu.
Wata ƙungiya mai rajin yaqi da harkar ƙwacen waya a Kano mai laƙabi da Youth Against Phone Snatching (YAPS) ta buƙaci Rundunar ’Yan Sanda ta Jihar Kano ta ayyana masu harkar ƙera makamai na musamman da ake amfani da su wajen cutar da mutane yayin faɗan daba da ƙwacen waya, cikin rukunin mutanen da ke taimakawa fashi da makami.
A wani taron gaggawa da ƙungiyar ta kira a ɗakin taro na PR Nigeria da ke Ƙofar Famfo a cikin birnin Kano, shugaban ƙungiyar Abdulwahab Sa’id Ahmad ya bayyana buƙatar gwamnati da Majalisar Dokokin Jihar Kano su ayyana masu amfani da makami suna ƙwacen waya a matsayin ‘yan fashi da makami, tare da zartar musu da hukunci daidai da ’yan fashi da makami kamar yadda doka ta tanada a tsarin dokokin Jihar Kano da ƙasa baki ɗaya.
Ƙungiyar ta kuma nemi gwamnati ta umarci Hukumar Tace Finafinai ta Jihar Kano, da ta dakatar da masu shirya finafinan Hausa a jihar daga shirya finafinai masu nuna yadda ake ta’addanci da gurɓata tarbiyya domin yadda irin waɗannan finafinan suke taka muhimmiyar rawa wajen gurɓata tarbiyyar matasa da kuma nuna dabarun ƙwacen waya da sauran laifuffuka.
Shugaban ƙungiyar har wa yau ya ja hankalin ’yan siyasa da su ji tsoron Allah a kan gudunmawar da suke bayarwa wajen daƙile ƙoƙarin da hukumomin gwamnati ke yi na yaƙi da yaɗuwar aikata manyan laifuka, wanda a cewar shugaban yin hakan babban koma baya ne ga tarbiyya da tsaron al’ummar Jihar Kano.
Kamar yadda ake ta kiraye kiraye ga hukumomi nima zan ƙara da tawa muryar bisa wannan dama da na samu, domin jan hankali gwamnati da hukumomin da abin ya shafa su ƙara daukar muhimman matakai na zamani don shawo kan wannan matsala, da ya haɗa da samar da na’urorin ɗaukar hoto a manyan hanyoyi da ƙanana, don su riqa naɗar abubuwan da ke gudana. Sannan a ƙara ɗaukar masu aikin sa-kai da za su taimakawa jami’an tsaro wajen aikin sintiri a cikin gari da lunguna, don hana ɓatagari sakat a dukkan mavoyarsu, musamman kamar ‘yan banga da ƙungiyoyin da suke da ƙwarewa a harkar tsaro.
Sannan su ma jama’a a cikin unguwanni su kafa ƙungiyoyin taimakon kai da kai na tsaron unguwannin su da iyalansu. Kuma a taimaka musu da gogewa da horon da suke buƙata. Mun sani gwamnati ba ta da jami’an tsaron da za su iya tsare dukkan al’umma a ko’ina, tilas sai da sa hannun jama’a, kamar yadda yake faruwa a wasu sassa na duniya.
Har wa yau, su ma sauran jama’a ina mai ƙara ba su shawara su daɗa ɗaukar dabaru da hikimomi na yadda za su yi wa kansu rigakafi. Ka samu wata matacciyar wayar android ka saka a aljihun ka ko jaka idan mace ce, ana iya samu a kasuwannin sayar da wayoyi da sauran wuraren gyaran waya. Haka kuma idan kana cikin mota ko A Daidaita Sahu, da zarar an ƙaraso wajen cinkoson ababen hawa to, ka voye wayarka ta ainihi. Ka daina danne danne ko kiran waya.
Idan kana tafiya sai ka hango zugar yara ‘yan daba masu alamun ‘yan fashin waya ne to, ka zama cikin shiri, ta lalubo matacciyar wayarka a kusa, sannan kuma ka nutsu sosai kar ka nuna musu alamun tsoro ko rikicewa. Don su ma mafi yawanci a rikice suke, kuma cikin maye. Idan sun buƙaci ka ba su wayarka sai ka miqa musu wannan tsohuwarwayar, don su qyale ka da lafiyar ka. Ko da ma ainihin wayarka ce mai kyau tsautsayi ya sa suka gani, ka basu kawai, kada ka yi gardama da su, rayuwarka ta fi maka wannan wayar muhimmanci.
Ka kiyaye bin hanyar da take da duhu ko wacce ƙafa ta ɗauke, saboda vata gari. Kuma idan ka samu kan ka a cikin taron jama’a tabbatar ka sa wayarka cikin aljihun wando, yadda kafin wani ya sa hannu ya lalube maka ita, ka ankara da shi.
Ya Allah ka shirya mana ‘yan uwan mu da suka kauce hanya. Ka tsare tarbiyyar mu da imanin mu da rayuwar mu, daga sharrin miyagun mutane. Ka hana su ganin mu, Ka raba hanya tsakanin mu da su. Amin.