Idan ɓera da sata: Abinda ke hana wasu matan kwalliya

Daga AMINA YUSUF ALI

Assalamu alaikum sannu ku da jimirin karatun jaridarku mai farin jini ta Manhaja. A wancan makon mun kawo muku bayani a kan yadda kwalliyar mata take da matuƙar tasiri a cikin gidan aurensu. Amma kuma mun samu ƙorafi da dama daga ‘yanuwa mata suna nuni da cewa, idan fa ɓera da sata, to daddawa ma fa tana wari. Wato ba fa mata ne ba sa son su gyara ba, har da laifin mazajensu. Haka su ma mazan wasu sun kira sun nuna cewa, ai ba kwalliya ce kaɗai ke jan ra’ayinsu ga mata ba. Akwai sauran abubuwa da idan mace na yi musu ko da tana kwalliyar sai abin ya hana kwalliyar yin tasiri a ciki. Don haka muke fatan mu kwance wa masu karatu wannan sarƙaƙiya. Domin to da ma ai shi ne amfanin ba da ƙofar tattaunawa tsakaninmu. Domin a samu damar shawarwari da tsokaci, da sauransu.

To amma fa ko da ba mu samu wannan ƙorafin ba da ma, wannan fili an san shi da haɗawa da dukan taiki koyaushe bayan an daki jaki. Wato kowanne ɓangare ana taɓowa. A sha karatu lafiya.

Abinda muka faɗa a wancan makon shi ne, yin kwalliyar mata tana da matuƙar tasiri a wajen inganta zaman aurenta tsakaninta da mijinta. Musamman idan aka yi la’akari da cewa kwalliya tana ɗaya daga cikin dalilan da suke ƙara danƙon soyayya tsakanin ma’aurata.

Amma Bahaushe ya ce, idan an bi ta ɓarawo, to sai a bi ta ma bi sawu. Sannan kuma idan ɓera da sata, to daddawa ma fa akwai ta da mugun wari. Abin nufi, ƙarfe ba ya ƙara shi ɗaya. Wato ma’ana dole ba wai haka kawai wasu matan suke ƙulla gaba tsakaninsu da kwalliya ba. Akwai wasu dalilai da suke kai wa ga haka. Ga wasu da wasu mata suka faɗa da bakinsu:

Maza ba sa saya wa matansu kayan ado: Wasu mata sun bayyana cewa, maza ba sa saya musu kayan ado da kwalliya wanda za su gyara. A cewar wasu matan ma rabon da mijin ya saya musu kayan kwalliya tun na lefenta. Da suka ƙare sai ya bar ta da saye. Sutura kuwa, sai sallah ko idan ta haihu. Wani ma ba ya yi mata na sallar ko na haihuwar. Ballantana su turare da man wanke kai da na kitso. Wani fa ko kuɗin kitso ba zai ba ta ba. Ya za a ganta fes-fes ita da yaranta? Kuma ya manta da yadda ya ɗauko ta tsaf daga gaban iyayenta sun saya mata komai ta yi kyau ka gani, ka yi sha’awa, kuma ya aura. Amma ya kasa ci gaba da tattala ta kamar yadda ka gan ta a baya.

Rashin cima mai kyau: Wasu kuma suna ganin cima mai kyau ita ce sirrin da za ta sa mace ta samu nutsuwa har ta iya yin kyau ta yi ɓul-ɓul, sannan ko kwalliya aka yi ta hau ta zauna. Musamman idan tana da ciki ko tana shayarwa. Rashin cin mai kyau kan sa mace ta zabge ta lalace ta zama tamkar tsohuwa. Ka tuna fa iyayenta da ba su ciyar da ita cima mai kyau tun daga haihuwarta har lokacin daka gan ta ba, da ba ka yi sha’awar ka aure ta ba. Kar ka manta ba don sun gaji da ita aka yi maka kyautar mutum sukutum ba. Ba don shari’a ba ma, ka san ba ka isa ka mallake ta ba. Don Allah a dinga tunawa da haka.

Wahalar rayuwa: Duk da dai mun san aure bauta ce, kuma aikin da mace take yi a gidan aure, Allah ne kaɗai zai biya ta. Amma mu sani, aikin gida da haihuwa shi yake sa mace ta yi saurin tsufa. Sannan idan aka yi rashin sa’a ba ta gyarawa, sai ta dawo wata iri.

Ka duba fa ka gani. Ta tashi tun safe. Ita ce girki, wankan yara da shirya su makaranta, abin karyawa, abincin makaranta, wanki wanke-wanke shara, wanke banɗaki, da sauransu. Ga haife-haife, dole ta jigata. Sai namiji ya fara gudunta ya dinga hangen sabon jini. Amma ‘yammatan da yake hangowa a waje, su ma da zai auro su, su sha wahalar da take sha, su ma haka za su dawo ko su fi ta rakwakkwaɓewa ma.

Maza su sani. Mace tamkar abin hawa take, sai da sabis. Ba yadda za ka ajiye ƙarfen nasara ka ce ba za ka dinga yi masa sabis ba ka ce zai yi ƙarko. Sai kana ba ta kulawa sannan za ta kasance kullum cikin yanayi mai kyau. ƊAn kuɗin ƙunshin nan, na kitso da sauran abubuwa. Ka yi mata sutura dai-dai ƙarfinta.

Rashin sana’a da aikin yi: Wasu matan ko sun yi niyyar gyarawar rashin ‘yan canji shi yake musu cikas. Ita kwalliya sai da kuɗi. Idan ba ta da shi, kuma maigida bai ba da ba, ko ba shi da halin badawa ai ba dama a yi. Haka rashin kuɗi a hannu yana sa ta damuwa da tunani kuma yana saurin tsufar da mace. Shi ya sa ma gara namij ya bar matarsa ta yi sana’a duk ƙaruwarsu ce. Ko ba komai za a gan ta da yaranku fes-fes. Ka ga ko ba komai idan aka ga iyalinka a mummunan yanayi mutuncinka zubewa yake yi.

Halin ko in kula na wasu mazan: Mata sun bayyana cewa, wasu mazan suna nuna ko in kula. Su kansu mazan ba sa wanka a kai-a kai, sannan ba sa gyara. Duk yadda aka yi musu kwalliya ba ya hana su kallo da hangen wasu matan a waje. Shi ya sa su ma suke zubar da batun kwalliyar suke rayuwarsu kawai.

Rashin yabawa da kyautatawa daga maza: Haka wasu matan sun bayyana cewa, rashin yaba kwalliyarsu da maza ke yi shi yake kashe musu gwiwa. Sai a yi kwalliya, amma sai ya yi kamar bai san kina yi ba. Haka sai ta sha kwalliya amma shi kuma sai ya ƙi dawowa da dare har sai ta yi bacci ko kuma kwalliyarta ta tuje ta goge. Shi ko yana can majalisa.

Amma ni a ganina wannan ba hujja ba ce. Domin maza da ma suna da ɗabi’ar nan ta nauyin baki. Don ba na so na ce ji-ji da kai. Wani ko bai faɗa ba ma ya yaba a cikin zuciyarsa. Ki cigaba da yi ai don Allah kike yi. Kuma wajen Allah kike neman lada. Wani yadda za ki gane yana yabawar, sai idan ba ki yi ba, sai ki ji yana ƙorafin me ya sa ba ki yi ba.
 
Kai kuma Yayana, meye a ciki idan ka yaba wa matarka kwalliyarta? Me zai ƙare ka, ko ya rage ka? Kamar ka ce kai kin yi kyau. Ko ka nuna dai wata alama ta yabawa, ko ka yi mata ihsani na kuɗi. Hakan zai ƙarfafa mata gwiwa. Wata fa kuɗinta kenan ta kashe ta yi sabon ɗinki, ko lalle ko ta sayi rigar bacci don ta birge ka.

Meye ciki, don ka ganta da lalle ka kama hannunta ka kalla ka ce gaskiya ya yi kyau. Ko ka kalli fuskarta da ta sha kwalliya, ka ce masha’Allah! Kin yi kyau, sanyin idaniyata. Wallahi waɗannan kalamai sai sun yi ta yi mata daɗi har tsahon rayuwarta. Wata ma ranar ba za ta iya bacci ba, saboda murna. Kuma ka ƙara mata ƙwarin gwiwar da za ta sa kullum ta yi ta tunanin hanyoyin da za ta bi don ta ƙara faranta maka rai, yadda ka faranta nata.

Amma fa gaskiya ba a taru an zama ɗaya ba. Wasu mazan tabbas suna yabawa. Amma a gaskiya kaɗan ne ainun a daga cikin mazan Hausawa.

Wasu mazan ma sai su dinga ƙorafin wai matan Hausawa kaza-kaza. Ba sa gyarawa, gara matan Kanuri da shuwa da sauransu. Amma abinda za ka duba, duk fa wannan abunda suke taƙama da shi na kwalliya da turare da kayan ƙamshi dukkansu ma fa da kuɗinka kake saya. Me zai hana ka karkatar da kuɗin zuwa matar da kake tare da ita ka ga idan ba ta koma haka ba. Kuma sannan maza su sani duk mace, mace ce. Da za ka auro balarabiya ka bar ta ba gyara, wallahi ita ma sai ta rakwakkwaɓe ta fita hayyacinta. Don haka, maza a dinga dubawa. Idan babu ne an san babu tana gidan kowa. Amma kuma idan akwai, a yi dai-dai gwargwadon iyawa. 

Duk da waɗannan dalilai kuma, a ɓangaren maza wasu suna ganin kwalliya ba ita ce kaɗai take iya riƙe a gurin mace ba. Eh sun yarda cewa, ita ce abu na farko da za ta fara jan hankalinsu zuwa ga mace. Amma kuma halinta shi yake sa zamansu ya yi ƙarko.

Duk da cewa babban sinadari ce kwalliya, amma a ganin wasu sai an haɗa da wasu halayen kafin ta yi tasiri. Wasu suna ganin duk kwalliyarki ba iya girki ba iya tarbiyyar yara ga ɓata ran miji da raina shi. Ga rashin biyayya da wulaƙanci za su sa namiji ya ji sam kwalliyar ma ba za ta burge shi ba.

Gare ku masu karatu. Sai ku yi mana alƙalanci. Mu na godiya ga masu kiran waya a yi mana fatan alkhairi da ba mu shawara. Haƙiƙa ku na ƙarfafa min gwiwa sosai. Na gode.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *