Daga UMAR GARBA a Katsina
Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta (INEC) reshen Jihar Katsina, ta ayyana ranar 14 ga watan Afrilu, 2023 a matsayin ranar da za a sake gudanar da zaɓen wasu ƙananan hukumomin jihar guda uku da suka haɗa da Kankia da Ƙanƙara da kuma Kurfi.
Hukumar ta bayyana cewar zaɓen da aka gudanar a ƙananan hukumomin da lamarin ya shafa a ranar 18 ga watan Maris, 2023 bai kammalu ba, saboda haka ne aka sake saka ranar da za a kammala su.
INEC ta ce, dokokinta ne suka yi tanadin sake gudanar da zaɓe a rumfuna ko mazaɓun da aka samu hargitsi.
Za a gudanar da zaɓen ne a rumfuna shida daga mazaɓu biyar da ke Ƙaramar Hukumar Kankia, rumfuna 17 a mazaɓu tara na Ƙaramar Hukumar Ƙanƙara da kuma rumfuna takwas a mazaɓu shida na Ƙaramar Hukumar Kurfi.