Daga BASHIR ISAH
Mataimakin shugaban Jami’ar Jihar Nasarawa da ke Keffi (NSUK), Farfesa Suleiman Bala Mohammed, ya yi kira ga sabbin ɗaliban da suka samu gurbin karatu a jami’ar da su kasance masu ɗa’a a kowane lokaci saboda a cewarsa, jami’ar ba za ta lamunci kowane nau’i na rashin ɗa’a ba.
Farfesa Suleiman ya wannan kira ne a wajen bikin rantsar da sabbin ɗalibai su 6,323 na shekarar karatu 2020/2021 da jami’ar ta shirya ta kuma gudanar a dandalin taron yaye ɗalibai a Juma’ar da ta gabata.
Jagoran ya kuma gargaɗi ɗaliban da su ƙaurace wa mu’amala da ƙungiyoyin asiri a ciki da wajen makaranta, tare da ja musu kunne a kan kada su bari a ruɗe su da shiga irin waɗannan ƙungiyoyi.
Haka nan, ya buƙaci ɗaliban da kada su yi jinkiri wajen kai rahoto ga shugaban sahshen kula da harkokin ɗalibai ko ga jami’an tsaron jami’ar a duk lokacin da suka gano take-taken ‘yan ƙungiyoyin asiri a cikin makarantar.
Ya ce shirin kwarmato na jami’ar ya taimaka matuƙa wajen rage aukuwar rashin ɗa’a a tsakanin malamai da ɗalibai a faɗin jami’ar.
Daga nan, ya yi kira ga sabbin ɗaliban da su shiga a yi wannan yaƙi tare da su wajen tsaftace jami’ar daga munanan ɗabi’u don samar da shugabanni nagartattu.