Kowa ya samu cigaba ya tuna da ɗan uwansa

Daga CMG HAUSA

Yau rana ce ta yaki da zazzaɓin cizon sauro Malariya. Wannan cuta tana haifar da mummunar barna a duniya. A cewar hukumar lafiya ta duniya WHO, mutane miliyan 241 sun kamu da cutar a shekarar 2020, yayin da wasu dubu 627 daga cikinsu sun mutu. Kana yawancin mutanen da suka kamu da cutar, da wadanda suka rasa rayuka sakamakon cutar, ‘yan ƙasashen Afirka ne.

Ƙasar Sin ita ma ta yi fama da cutar Malariya sosai a baya. A shekarun 1940, ƙasar Sin ta kan sanar da kamuwar mutane kimanin miliyan 30 da Malariya a duk shekara. Sai dai zuwa yanzu, an riga an kawar da cutar daga ƙasar Sin: A shekarar 2021, bayan da ba a samu ko da mutum daya da ya kamu da cutar ba a ƙasar cikin wa’adin wasu shekaru 4 a jere, ya sa ta samu tabbaci daga hukumar WHO cewa, an yi nasarar kawar da cutar baki daya cikin ƙasar.

Ta yaya ƙasar Sin ta cimma wannan nasara? Amsar ita ce ƙoƙarin ɗaukar dabaru masu dacewa a kai a kai. Wasu shekaru 50 da suka wuce, masu nazarin kimiya da fasaha na ƙasar Sin sun gano sinadarin Artemisinin, inda suka fara sarrafa magani da shi. Zuwa yanzu magunguna masu ƙunshe da Artemisinin sun zama dabara mafi kyau da ake yin amfani da ita wajen jinyar mutanen da suka kamu da cutar Malaria. Kana ƙasar ta dauki wasu matakai irinsu raba gidan sauro, da fasahohi na kashe sauro, don dakile cutar Malaria.

Abokai da suka fahimci manufofin ƙasar Sin a fannin hulda da ƙasashen waje sun san cewa, ƙasar Sin ba ta yin babakere a fannin fasahohi don kare moriyar kai. Bayan da ƙasar ta samu fasahohin da ake buƙata wajen daƙile cutar Malaria, ta fara taimakawa ƙasashe masu tasowa, ta hanyar ba su magunguna, da tura musu ƙwararrun likitoci, da horar da ma’aikata, da dai sauransu.

Daga shekarar 2012 zuwa yanzu, ƙasar Sin ta aiwatar da manyan ayyuka na tallafawa sauran ƙasashe fiye da 300, da gina cibiyoyin daƙile yaɗuwar Malaria kyauta a ƙasashe 30, da tura ƙwararrun likitoci dubu 28 zuwa ƙasashe da yankuna 72, inda aka horar da ma’aikata masu fasahar daƙile cutar Malaria fiye da dubu 10.

A ƙasar Sao Tome da Principe, a kan samu mutane dubu 2 zuwa 3 da suka kamu da cutar Malaria a kowace shekara. Sai dai, yanzu haka, wata ƙungiyar likitoci ta kasar Sin tana gudanar da aikin daƙile cutar a cikin wasu kauyukan kasar. A safiyar kowace rana, likitocin Sin da abokan aikinsu ‘yan ƙasar Sao Tome da Principe su kan shiga ƙauyukan, don gudanar da gwajin jinin mazauna ƙauyukan. Idan an ga mutum ya kamu da cutar Malaria, za a ba shi magani don ya sha nan take.

Sa’an nan zuwa dare, za su shiga dajin dake kewayen ƙauyukan, inda za su fesa ruwan magani don kashe sauro. Ta waɗannan dabaru, sannu a hankali aka fara shawo kan yanayin yaɗuwar cutar Malaria a ƙasar.

Sai dai me ya sa ƙasar Sin ke son raba fasahohinta na daƙile cutar Malaria tare da sauran ƙasashe? Dalili shi ne, ƙasar Sin na da manufar kafa al’ummar dan Adam mai kyakkyawar makoma ta bai ɗaya, wadda ta sa take lura da buƙatu na sauran ƙasashe, musamman ma a fannin raya ƙasa. A ganin ƙasar, idan ita kaɗai ta samu ci gaba, to buƙatarta ba ta biya ba, kana kowa ya samu ci gaba ya tuna da dan uwansa.

A wannan lokaci na watan Ramadan mai tsarki, ya kamata mu yi addu’a da fatan Allah ya sa mu amfana da juna, da fatan za mu kawar da cutar Malaria a ko ina cikin sauri.

Mai Fassara: Bello Wang