Kuɗin intanet: Majalisa ta gayyaci shugaban CBN don ya yi ƙarin haske

Daga FATUHU MUSTAPHA

Gwamnan Babban Bankin Nijeriya (CBN), Godwin Emefiele, ya bayyana a gaban Majalisar Dattawa domin kare batun haramta hada-hadar kuɗaɗen intanet (crypto currencies) da gwamnati ta yi.

Majalisar ta gayyaci Emefiele ne domin ya yi mata ƙarin haske kan irin damarmaki da kuma haɗarin da ke tattare da harkar kuɗaɗen intanet ga tattalin arzikin ƙasa.

A can baya, Babban Bankin, ta hannun Daraktan Sashen Sanya wa Bankuna Ido Bello Hassan, ya bayyana cewa waɗannan kuɗaɗe na intanet wasu da ba a san ko su wane ne ba suke bada su kuma ba tare da wasu sanannun dokoki ba.

Hassan ya ce ana yawan amfani da waɗannan kuɗaɗe wajen aiwatar da haramtattun harkoki, ciki har da zambar kuɗaɗe, sayen makamai da sauransu. Sai dai, wasu ‘yan majalisu na ra’ayin cewa ya kamata a duba lamarin sosai.

Tare da cewa yayin da kuɗaɗen na intanet ke tattare da matsaloli, amma kuma jarkar ta zama hanyar da ta fi kowace saurin bunƙasa a fagen hada-hadar kuɗaɗen a faɗin duniya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *