Kwaɓa da harigido ne matsalar mawaƙan wannan zamani – inji Baban Khausar

Daga AISHA ASAS

Malam Sagir Baban Khausar shahararren mawaƙin Hausa wanda waƙoƙinsa suka fi mayar da hankali fannin ilimantarwa, faɗakarwa da nuni cikin nishaɗi. A wannan makon jaridar Manhaja ta samu damar tattaunawa da shi don kawo wa masu karatu wani abu da ba su sani ba game da shi. Ga dai yadda wakiliyar ta tattauna da shi:

Mu fara da jin tarihin ka.
Assalamu alaikum. Da farko dai suna na Sagir Mustapha Ɗanyaro, jama’a sun fi sani na da Sagir Baban Kausar. Ni haifaffen Lungun Liman ne da ke gidan Liman a Kabala Coastain da ke ƙaramar hukumar Kaduna ta Arewa a jihar Kaduna. Kuma an haife ni ne a ranar 01/10/ 1980. Da yake gidan namu gidan malamai ne, na fara da karatun addini kamar kowane yaro a wannan zuri’a kuma na yi karatun boko daga firamare har zuwa makarantar gaba da sakandare. Ina da matsayin karatu na NCE, sannan na halarci kwasa-kwasai ciki da wajen ƙasar nan. Na taɓa aiki a BAT da EMCON duk a garin Zaria. Yanzu haka ina koyon aikin Jarida ƙarƙashin wani kamfani mai zaman kansa Iman Ventures and Communication Nig Ltd a nan garin Kaduna. Ina da mata ɗaya da yara uku.

Shin kana rubuta waƙarka ne, kafin ka shiga sutidiyo ko kuwa kana shiga situdiyo ta ke zubowa daga ƙwaƙwalwar ka?
Haƙiƙa ina rubuta waƙa ne kafin in rere ta, saboda hakan ne ke ba ni damar nazartar abin da nake so in yi magana a kai.

Ka kasance mawaƙi mai cike da hikimomi a waƙarka, shin kana dogon nazari ne ko bincike kafin ka fitar da waƙa?
Wannan gaskiya ne duk lokacin da ka ke son samar da nagartaccen saƙo zuwa ga al’umma dole ne ka yi nazari mai zurfi kafin ka samar da waƙa. Hakan ya ba ni damar mu’amala da manya farfesoshi da daktocin Hausa a jami’o’i da dama a ciki da wajen ƙasar nan kuma ya ba ni damar sayen littattafai da dama wanda suke bayani a kan Harshen Hausa da Hausawa, da kuma littattafai da aka rubuta su a kan fannoni da dama na rayuwa da na Addini. Yin hakan ke ba ka damar yin waƙa kanka tsaye. Sannan kuma a kodayaushe mawaƙi na fuskantar tambayoyi daga jama’a musamman ɗaliban Ilimi masu nazartar Harshen Hausa.

Yaushe ka fara waƙa?
 Na fara waƙa ne tun daga Islamiyya da waƙoƙin Maulidi da makamantan su har ta kai ga muna fita yawon majalisai na yabon Ma’aikin Allah (SAW).
Na bi Marigayi Shariff Rabi’u Usman Baba, na bi Malam Bashir Ɗanmusa, na bi Malam Musa Palladan Zaria wanda yanzu haka shi ne babban limamin masallacin Juma’a na Palladan. A wuraren shekarar 2000 ne na fara leƙa taskar waƙoƙin faɗakarwa da fina-finai, sakamakon mafi yawancin wanda suka fara fim ɗin Hausa a Kaduna ‘yan Kabala Costain ne kuma wasu iyayenmu ne wasu kuma yayyinmu.
Daga leƙe sai ga mu ciki tsundum. To har zuwa yanzu dai ga mu a ciki, don haka za ki ga ina ɗauka kowanne daga fannonin waƙar ina taɓawa. Musamman lokacin da wani abu ya faru da ya shafi ɓangaren.

Me ya ja ra’ayinka zuwa wannan harkar ta waƙa?
Kamar yadda na faɗa a baya mun fara ne daga waƙoƙin yabon Ma’aiki (SAW) a lokacin babu mawaƙan fim da yawa, shi ne su ‘yan fim wanda na faɗa miki iyayenmu ne da yayyenmu sai suka rinƙa nuna mana ko za mu yi musu waƙar fim, fim ɗin da na fara ma waƙa shi ne ‘Duhun Dare’; da na yi kowa ya ce waƙa ta yi shi kenan kuma sai na ci gaba da yi musu.

Ka koya ne ko kai ɗan gado ne?
 Ban gaji waƙa ba gaskiya, koyon ta na yi tun da ni gidanmu gidan malamai ne, amma kar ki manta da yawan littattafan Addini ma da waƙa aka rubuta su.

Za mu iya sanin nasarorin da ka samu?
Haƙiƙa nasarori ba sa misaltuwa domin duk wani mutum da ya isa da ɗaukaka a ƙasar nan da makwabta waƙa ta haɗa ni da shi ko a vangaren mulki ko ilimi ko kasuwanci da sauransu. Duk wani wurin alfarma waƙa ta kai ni. Duk wata dama da ɗan adam ke nema waƙa ta ba ni, Alhamdu lillah.

A kwai ƙalubale?
 A kowane al’amari na rayuwa akwai ƙalubale, haka ita ma waƙar, su ma mun gamu da iri daban-daban kuma Allah cikin ikonSa Ya ba mu kariya da kuma shi zamani na tafiya da mu.

Baban Khaisar

A wannan zamani da yawa a mawaƙa suna son ransu ne, ba tare da sun san ƙa’idojin ingantacciyar waƙa ba, hakan ya haifar da yawaitar gurɓatattun waƙoƙin Hausa. Shin a matsayinka na ɗaya daga cikin mawaƙan da basirarsu ta kai a kira su manya a harkar, akwai wani shiri da kuke yi na ganin an ilmantar da ire-iren waɗannan sababbin mawaƙa?
Wannan gaskiya ne mun riski zamani da wata waƙar ba za ka so ka ji ta tare da mutane ba saboda harigido da kwaɓar da ke ciki. To amma ɗaukar mataki ko ɗabbaƙa wani tsari da zai kawo ƙarshen faruwar hakan ya na da wuya a halin da mu ke ciki a yanzu domin kamar yadda ki ka sani ne wannan al’umma ta mu zama ake irin wanda ake cewa kara zube, babu wani shinge ko ƙofa da za a ce ita za a bi sannan a shigo sana’ar.
Mun yi yinƙurin kafa ƙungiyoyi domin tsarkake sana’ar da kuma koya wa ‘yan baya ƙa’idoji da tsaren-tsaren waƙa da rabe-raben ta amma ciwon shugabanci ya hana komai tafiya domin a wani lokaci mun yi ƙungiyar NALSU wacce ta yi tasirin ban mamaki a Arewa sai da ta zama ita kaɗai ce inuwar da ke haɗa mawaƙa waje ɗaya, a ƙarshe ta yi ƙarkon kifi saboda kokawar shugabanci.
Haka mun zo mun shirya tafiyar Ranar Mawaƙan Hausa Foundation wadda sai da ta yi tasirin da ta haɗa mawaƙan Hausa na gargajiya da na zamani daga wasu ƙasashen Afrika, kuma tafiyar ta samu karɓuwa ga sarakuna da wasu jami’o’in ƙasar nan da na ƙasashen waje, amma a ƙarshe cutar shugabanci ta rusa tafiyar. A yanzu haka sai in ce an koma gidan jiya kowa ya na rayuwar sa ne a qarqashin kansa da fahimtar sa.

Wace shawara za ka bai wa mawaƙa ‘yan’uwanka?
Shawara ta ga mawaƙa a kodayaushe mu ji tsoron Allah, mu jakadun al’umma ne kuma jakadun harshen Hausa ne, akwai haƙƙin Allah a kanmu akwai haƙƙin al’umma a kanmu, kuma ranar gobe ƙiyama Allah zai tambaye mu yadda muka tafiyar da fasahar da Ya albarkace mu da ita.

Ka taɓa samun karramawa a fagen waƙa?
Na amshi karramawa daga wurare daban-daban, jami’o’i da kuma tsangayun fahasa da wasu ƙungiyoyin Hausa. Akwai kuma wanda na shiga gasar rubutu ko rera waƙa ne na yi nasarar samun su.

Madalla mu na godiya.
Masha Allah, ni ma haka kuma ina miƙa saƙon jinjinata ga duk masu bibbiyar waƙoƙina a ko’ina suke tare da sauran al’umma, ina yi wa kowa fatan alheri. Na gode.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *