Kwamitin sulhun MƊD ya yi kira da a ƙara ƙaimi wajen inganta ƙwarewa a Afirka

Daga CMG HAUSA

Kwamitin sulhu na MƊD ya yi kira da a ƙara daidaita tsarin hadin gwiwa a tsakanin dukkan abokan hulɗa masu ruwa da tsaki, musamman ta hanyar inganta ƙwarewa wajen tinkarar matsalar tashe-tashen hankula, da wanzar da zaman lafiya da sauran ƙalubale a nahiyar Afirka.

A cikin sanarwar da shugaban kwamitin sulhun majalisar na karɓa-karɓa na watan Agusta, kana zaunannen wakilin ƙasar Sin a MƊD Zhang Jun ya gabatar, kwamitin mai wakilai 15 ya amince da buƙatar ƙara karfin ƙwarewar ƙasashen Afirka yadda ya kamata, da haɗa kai, da daidaita al’amura, da matakan da suka dace da yanayin kowace ƙasa da yanki.

Kwamitin ya kuma jaddada muhimmancin mutunta ikon mulkin kai da jagorancin ƙasashen Afirka, da kuma tallafa musu wajen inganta tsarin doka, da ƙarfafa hukumomin kasa, da gina tsarin shugabanci na-gari, da yayata da kare haƙƙin dan Adam, da sauransu.

Ya kuma jaddada buƙatar raba dabaru, da samar da tallafin kuɗaɗen kan yayata matakan kwance ɗamara, da sake dunƙulewa, ciki har da waɗanda suka shafi saki da sake haɗewar yaran da ke da alaƙa da shiga aikin soja ko ƙungiyoyi masu ɗauke da makamai, da kuma sake fasalin ɓangaren tsaro, bayan yanayi na rikici, don tabbatar da zaman lafiya, da kwanciyar hankali da tsaro na bai ɗaya.

Mai fassara: Ibrahim Yaya

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *