LEAD ta nemi INEC ta tsawaita rajistar katin zaɓe zuwa Disamba

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

Ƙungiyar ‘Leadership and Entrepreneurship Advocacy’ (LEAD), wata ƙungiya mai zaman kanta, ta buƙaci Hukumar Zave Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC), da ta tsawaita rajistar katin masu kaɗa ƙuri’a zuwa Disamba.

Babban Darakta na LEAD, Chukwuma Okenwa, ne ya yi wannan kiran a wata hira da kamfanin dillancin labarai na Nijeriya, a Enugu ranar Laraba.

Okenwa ya yi magana kan yadda ake samun ƙaruwar sabbin masu rajista, da zanga-zangar da wasu matasa suka yi a faɗin ƙasar, kan rashin isassun injinan katin zaɓe da za su iya kai wa ga kowa a kullum.

A cewarsa, har sai INEC ta samu adadin masu kaɗa auri’a da za su shiga duk tsarin dimokuraɗiyya, kuma ya yi daidai da yawan al’ummar ƙasar, ya kamata hukumar ta ci gaba da ragistar katin zave ko da bayan babban zaɓen 2023.

Ya tunatar da hukumar INEC aikin kafa ta, wanda ya ƙunshi haɗa kai, ya ƙara da cewa, “Babu wani dalili da za a hana duk wanda ya gabatar da kansa don a yi masa rajista.”

“Har sai mutane sun yi ƙaranci a kowace cibiyar rajista, to zai zama dalili mai kyau na kawo ƙarshen aikin, amma a wannan yanayin, akwai dubban ‘yan Nijeriya da ke fatan samun katun zaɓe a kullum.

“Don haka zan ba da shawarar cewa a ci gaba da gudanar da aikin har zuwa watanni biyu kafin zaɓe, ta yadda miliyoyin ’yan Nijeriya ba za su yi wa kansu hakkinsu ba,” inji shi.

Okenwa ya kuma buƙaci INEC da ta yi la’akari da abubuwan da suka faru a rumfunan zaɓe da dama a faɗin Nijeriya, inda jama’a, musamman matasa, ke fitowa ƙwansu da ƙwarƙwata, a kullum, domin yin rajista, ta hanyar tinkarar ƙalubale kamar rashin isassun injinan rajista, don tabbatar da cewa an bai wa zaɓaɓɓun damammaki don gudanar da ayyukansu na jama’a.

“Injunan rajistar CVR ba su isa ba; da yawa sun yi takaici saboda sun fito yin rajista, amma sun dawo gida bayan sun shafe tsawon yini ba tare da sun cimma burinsu ba.

“Don haka hukumar a koda yaushe, yakamata ta motsa ko kuma ta tsawaita wa’adin,” in ji shi.

Sai dai shugaban cibiyar sadarwa ta LEAD, ya yabawa mashahuran mutane da masu fasaha kan yadda suke wayar da kan ’yan Nijeriya musamman matasa don samun katin zaɓe.

Okenwa ya ƙara da cewa, “Akwai shaidun da ke nuna cewa duk wani matashi kuma ɗan Nijeriya mai ma’ana a yanzu yana son tsarin ƙasar ya yi aiki.”

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *