Ma’aikata da sarakuna na fuskantar barazana kan zaɓen ƙananan hukumomi a Kebbi

Daga JAMIL GULMA a Kebbi

Yayin da ake dab da gudanar da zaɓen ƙananan hukumomi ranar Asabar, wacce ta yi daidai da 5 ga Fabrairu, 2022, a Jihar Kebbi, a na zargin ma’aikatan gwamnati da sarakunan gargajiya na fuskantar barazana daga waɗansu ƙusoshin jam’iyyar APC mai mulki a jihar da ke goyon bayan ɓangaren Gwamna Atiku Bagudu.

Kwana-kwanan nan dai abin da ya fi ɗaukar hankulan jama’ar jihar bai wuce yaƙin neman zaɓe da ake yi da ya mamaye shafukan sada zumunta na zamani ba, inda aka ji shugaban kwamitin amintattu na jam’iyyar APC na jihar Kebbi Alhaji Sani Zauro (Sani Hukuma) a garin Yauri yana umartar shugaban hukumar kula da ƙananan hukumomi da ya kori duk wani ma’aikacin ƙaramar hukuma da aka gano ba ya yi wa jam’iyya hidima.

Haka zalika a ƙaramar hukumar mulki ta Sakaba an ji Alhaji Nafi’u Mangalsin ɗaya daga cikin jagororin jam’iyyar ta APC ɓangaren Gwamna Atiku yana barazanar tuɓe rawanin duk wani basaraken da baya goyon bayan tafiyar su, da kuma korar duk wani ma’aikacin gwamnati da ba ya tare da ɓangaren su. 

“Duk wani ma’aikaci wanda ya yi kissa ko munafurci a tafiyar na rantse da Allah bakin kujerar  ɗan kan bura uba, Billahillazi La Ilaha Illahuwa duk basarake da ya yi wa wannan tafiyar karan-tsaye za mu cire rawanin sa,” inji shi.

A ɗaya ɓangaren na jam’iyyar APC wanda Maigirma Sanata Adamu Aliero ya ke jagoranci, bayan kammala wani taron jami’an gudanarwa da ‘yan takara da suka tsayar a ƙananan hukumomi 21 da ke faɗin jihar amma sai dai hukumar zaɓe mai zaman kanta ta jihar (KESIEC) ta ƙi karɓar takardunsu da lauyoyinsu suka miƙa ta janye kulluhin ‘yan takarar bisa ga dalilan rashin yi musu adalci.

Alhaji Abdullahi Muhammed Lamba Ɗanmasanin Yauri jagoran wannan ɓangaren ya bayyana wa wakilinmu da cewa sun ɗauki matakin shi ne rashin gaskiya da aka tafka wa ‘ya’yan jam’iyyar musamman magoya bayan ɓangaren Sanata Adamu Aliero.

Ya ƙara da cewa duk wanda ke goyon bayan ɓangaren Sanata Adamu Aliero ba zai shiga zaɓe ba kuma ba su fita don jefa ƙuri’a ba har sai idan an yi abinda ya kamata.

“Mu a hasashenmu Gwamna Atiku yana yi wa jam’iyyar APC zagon ƙasa, saboda ya raya jam’iyyar PDP saboda idan aka cire shugaban ma’aikata na gidan gwamnatin jihar Kebbi Alhaji Sulaiman Muhammad Argungu babu wani cikakken ɗan jam’iyyar APC a gwamnatin jihar, haka zalika kashi tamanin zuwa casa’in na masu riƙe da madafun iko a jihar duk ‘ya’yan jam’iyyar PDP ne waɗanda ya tarkato bayan sun faɗi zave,” inji shi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *