Manyan ƙalubalen da suke gaban bankunan Nijeriya a 2022

Daga AMINA YUSUF ALI

Rahotanni sun bayyana cewa, dole bankunan Nijeriya su ƙara zage damtse don tunkarar ƙalubalen da suke tunkaro su a cikin shekarar nan ta 2022. 

Ƙalubalen da suke fuskantar bankunan sun haɗa da rashin samun riba sosai, matsanancin haraji, gasa daga kamfanonin sadarwa, da kuma kamfanonin ba da rance. Waɗannan su ne ake ganin za su iya zama barazana ga Bankunan Nijeriya a shekarar nan. 

Waɗannan bayanai suna ƙunshe ne cikin rahoton da Renaissance Capital ta rawaito. 

Renaissance Capital kamfani ne na kasuwanci da al’amuran banki. 

A cewar majiyar tamu, bankunan Nijeriya ba su taɓa shiga cikin barazana irin wannan ba. Inda ya bayyana cewa, ko a shekarar 2021 bankunan sun fuskanci ƙalubale manya kamar yadda CBN ya dinga sakko da darajar Naira. Amma ba su kai ƙarfin waɗanda ake sa ran za su fuskanta a bana ba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *