Marubutan ‘online’ na fuskantar ƙalubale – Khadija Nanerh

“Ribar da marubuta suke samu tana da yawa”

Daga ABBA ABUBAKAR YAKUBU

Khadija M. Sha’aban, wacce aka fi kira da Nanerh, ‘yar mutanen Zazzau kamar yadda ake gani a rubuce-rubucenta, matashiyar marubuciya ce mai kaifin basira da himmar son rubuce-rubuce, duk kuwa da ƙarancin shekarunta. Tana daga cikin marubutan adabi na yanar gizo (online) da tauraruwar su ke haskawa, sakamakon irin salon rubutun da take yi da suka shafi tarbiyya da zamantakewa. A zantawarta da wakilin Blueprint Manhaja, Marubuciya Nanerh ta bayyana burin ta da yadda take hangen makomar harkar rubutun adabi a nan gaba. 

MANHAJA: Wacce ce Nana Khadija ‘Yar Mutanen Zazzau?
NANERH: (Murmushi) Sunana Nana Khadija Sha’aban, ni haifaffiyar garin Kano ce, mahaiyata bakanuwa ce ta asali, amma mahaifina bazazzagi ne. Na yi karatuna tun daga ajin rainon yara wato Nursery har zuwa sakandire. Yanzu haka ina da niyyar cigaba da karatuna, bayan na yi JAMB. 

Kina ɗaya daga cikin matasan marubuta da ke ƙoƙarin rubuce rubuce, ko za mu san abin da ya ja hankalinki ki ka fara rubutu?
Abinda ya ja hankalina na fara rubutun littafi shine, tun ina ƙarama ni ma’abociyar karance-karancen litattafan Hausa ce, kuma ina jin wanda ake karantawa na sauraro, a rediyo ko kuma ta YouTube, wannan dalilin ne ya sa nima na ji ina tsananin son na ga ina rubuta na wa littafin, don haka na faɗa cikin duniyar marubuta domin nima a dama da ni.

Ki kan yi rubutun ki ne a littafi ko ke ma ‘online’ kike fitarwa?
Tun da na fara rubutu a ‘online’ nake sake wa. Ban tava buga na littafi ba, amma ina da burin nan gaba idan dama ta samu in buga, saboda kowanne da muhimmancinsa.

Wacce riba marubutan ‘online’ suke samu daga labaran da suke sakewa ta waya, kuma wanne ƙalubale ke tattare da hakan?
Ribar da marubuta suke samu tana da yawa, domin ko a iya faɗakarwar da suke yi wa mutane ma, kaɗai suna samun riba, tare da tarin ɗimbin lada na sunnata aikin alheri da wani zai koyi da shi. Rayuwar mata, ina nufin ‘yan mata da matan aure tana inganta sosai ta dalilin irin waɗannan rubuce rubuce da muke yi. Sai dai kuma ƙalubalen da ke tattare da shi na masu satar fasaha. Domin sai ka ga marubuci ya wuni yana yin rubutu, amman abin takaicin sai wasu mutanen marasa imani su zo, su canza masa tsarin labarin, su canza sunan marubucin, wasu shahararrun ma har sunan littafin suke canzawa. Wannan ba ƙaramin ci mana tuwo a ƙwarya yake yi ba gaskiya. 

Yaya kike fitar da naki rubutun, kyauta ne ko na kuɗi ne kamar yadda wasu ke yi?
Babu wanda ba na yi, ina yin na kuɗi da kuma na kyautar. Kuma Alhamdulillahi babu laifi, ana samun amfani kuma masu karatun littattafai na suna ƙara min ƙwarin gwiwa sosai. Wasu ma a dalilin haka zumunci ya ƙullu sosai a tsakanin mu. 

Kawo yanzu littattafai nawa kika rubuta, kuma wacce nasara kika samu daga rubuce rubucen da kike yi?
Na rubuta litattafai guda goma, da suka haɗa da ‘Ƙaddarat, ‘Babana Ne Sanadi’, ‘Wurin da ba ‘Ƙasa’, ‘So Shu’umi’, ‘Sauyin Zuciya’, ‘Daren Aurena’, ‘Tsantsar Yaudara’ da ‘Bambamcin Aƙida’, sai kuma ‘Ni da Billy Ƙueen’, sannan da ‘Nasma’.

In sha Allahu zuwa bayan sallah, idan Allah ya kai mu, akwai wasu sababbin littattafan da nake son yi aiki a kansu. Har wa yau, kamar yadda na faɗa a baya na samu nasarori masu yawa waɗanda nake ganin sun fi min kowacce nasara ta abin duniya. Wato irin yadda masu bibiyar littattafai na suke min godiya da yadda wasu labaran da nake yi suke sauya musu rayuwa. Ina jin daɗi sosai na yadda makarantan littattafai na suke nuna min soyayyarsu, kuma suke ƙaunar salon rubutuna.

Ta yaya kike ganin za a kawo gyara da cigaba a harkar rubutun adabi?
(Dariya) To, ni dai a matsayina na ‘yar autan marubuta babban abin da nake burin gani a wannan harka shi ne a samu ƙaƙƙarfan haɗin kan marubuta wajen yaƙi da yaɗuwar rubuce rubucen batsa, da kawo ƙarshen masu satar fasaha. Ina ganin ta haka ne za a kawo gyara a harkar rubutun adabi.

Bangon littafin ‘Daren Aurena’

Wacce alaqa ke tsakanin ki da sauran marubuta, maza da mata, da ke ba da gudunmawa a wannan harka?
Gaskiya muna da kyakkyawar alaƙa sosai, don kamar yadda na gaya maka a baya, ina ɗaukar kaina a matsayin ‘yar autan marubuta, don ko da wanda na girma a shekaru to, kaɗan ne. Ina ɗaukar su a matsayin yayuna, ƙawayena, har ma iyayena, tunda harka ce da ta haɗo mutane daban daban. Ina matuƙar girmama su, muna kuma mutunci da kowa, musamman Waɗanda muke samun damar haɗuwa, muna zama mu yi raha da juna.

Idan abin ki bai wa marubuta shawara ne kan yadda za a inganta harkar rubuce rubuce, me za ki ce musu?
To, duk da dai yake ba wani daɗewa sosai na yi a harkar ba, amma ina son in ba mu shawara kan muhimmancin zurfafa bincike da yin tunani kan wasu matsalolin rayuwa, da za mu iya ɗauka mu yi rubutu a kai. Ba lallai ko yaushe ya zama rubutu a kan soyayya ko zaman aure ba. Akwai wasu ɓangarorin da nake ganin za mu iya shiga ciki, mu yi nazari kuma har mu kawo hanyoyin samar da gyara a ciki.

A ƙarshe, wacce karin maganar Hausa ce take tasiri a rayuwarki?
(Dariya) Abin da babba ya hango, yaro ko ya hau kan Dala da Gwauron Dutse ba zai tava hangowa ba.

Madalla, mun gode.
Ni ma na gode ƙwarai.