Mutum 3 sun mutu, da dama sun jikkata a mashaya

Daga BASHIR ISAH

Aƙalla mutum uku ne ake jin sun rasa rayukansu sannan wasu da dama sun jikkata a sakamakon fashewa mai ƙarfi da ta auku a ranar Laraba a yankin Kabba, Jihar Kogi.

Majiyar Kamfanin Dillancin Labarai na Ƙasa (NAN) ta nuna iftila’in ya auku ne a wata mashaya da ke daura da Mararrabar Lewu da ke cikin garin Kabba.

Majiyar ta ce fashewar ta auku ne da misalin ƙarfe 9:45 na dare a dadai lokacin da mashaya ke tsaka da shaye-shayensu.

A cewar majiyar, “Na ji wata ƙara mai ƙarfin gaske kusa da inda nake, ko da na isa wurin, sai na tarar da gawarwaki uku sannan an kwashi waɗanda suka jikkata zuwa asibiti.”

Wani ganau ya ce, “Bom ce ta tashi, saboda ƙarar fashewar mai rikitarwa ce, an samu asarar rai sannan wasu sun jikkata.

“Na ga yadda jami’an tsaro suka kwashi mutane zuwa asibitin Kabba,” in ji ganau ɗin.

Sai dai Kwamishinan ‘Yan Sandan Jihar, Mr Edward Ebuka ya shaida wa NAN cewar, rahotannin da suka samu sun nuna tunkunyar gas ce ta fashe ba bom ba.

Ya ce jami’ansu na ci gaba da gudanar da bincike kan lamarin, kuma zai ba da ƙarin bayani bayan kammala bincike.