Daga UMAR GARBA a Katsina
Wasu jiga-jigan jam’iyyar PDP tare da magoya bayansu 10,000 sun sauya sheƙa zuwa APC a Jihar Katsina.
Akasarin waɗanda suka kwashe kayansu daga jam’iyyar ta PDP zuwa APC na hannun daman tsohon gwamnan jihar ne, wato Ibrahim Shehu Shema.
Gwamnan Jihar Katsina, Aminu Bello Masari ne ya karɓe su a gidan gwamnatin jihar.
Sauya sheƙar na zuwa ne ‘yan kwanaki kaɗan kafin gudanar da zaɓen gwamnoni da na ‘yan majalisun jihohi a ranar Asabar, 11 ga watan Maris.
Daraktan yaƙin neman zaɓen ɗan takarar gwamnan Jihar Katsina Ahmed Musa Ɗangiwa ne ya bayyana wa manema labarai haka a Fadar Gwamnatin jihar.
Waɗanda suka sauya sheƙar sun haɗa da tsohon shugaban ƙaramar hukumar Kaita, Hon. Ibrahim Lawal Ɗankaba, wanda kuma shi ne tsohon shugaban ALGON reshen Jihar Katsina kuma tsohon sakataren ƙungiyar PDP shiyyar Arewa maso yamma, Bishir Tanimu Dutsin-ma wanda ya kasance shugaban Ƙaramar Hukumar Dutsin-ma, mamban kwamitin jam’iyyar PDP na jihar Katsina, tsohon sakatare/ma’ajin jam’iyyar PDP na shiyyar Arewa maso Yamma.
Sauran sun haɗa da wani ɗan kasuwa, Idris Kwaɗo da tsohon Kwamishinan Ma’aikatar Albarkatun Ruwa a mulkin Shema, Jamilu Manman Ɗan Musa da Abdulwahab Sani Stores wanda ya kasance mataimaki na musamman ga marigayi tsohon Shugaban Ƙasa Umaru Musa Yar’adua.
Sai kuma ‘yar takarar sanata a jam’iyyar PDP a Katsina ta tsakiya a zaɓen fidda gwani na jam’iyyar da ba ta yi nasara ba, Gimbiya Aisha Isa, da Tijjani Auwalu Mabo wanda shi ne shugaban Ƙaramar Hukumar Zango.
Waɗanda lamarin ya shafa sun bayyana cewar sun sauya sheƙar ne don taimaka wa ɗan takarar gwamnan jihar a jam’iyyar APC, Dikko Umar Raɗɗa samun nasara a zaɓen gwamnan da ke tafe.