Mutane 1,129 aka kashe a Kaduna shekarar 2021 – Gwamnatin Kaduna

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Gwamnan Jihar Kaduna, Malam Nasiru Ahmed El-rufa’i ya bayyana cewa hare-haren da ‘yan bindiga ke kaiwa a Arewa maso yammacin Nijeriya ya fi na Boko Haram muni.

El-Rufai wanda ke jawabi a wajen taron gabatar da rahoton tsaro na shekarar 2021, ya ce rahoton da aka fitar na bara ya tabbar da cewa akwai aiki gaban mahukunta.

Gwamnan ya ce ya kamata gwamnati ta ɗauki tsauraran matakan tsaro kan hare-haren ‘yan bindiga a Arewa maso Yamma fiye da yadda ta yi kan ‘yan Boko Haram.

Gwamnatin jihar Kaduna ta ce an kashe mutane 1,129 a faɗin jihar Kaduna a bara, sannan an kiyasta cewa kullum akan sace mutane tara a faɗin jihar.

Rahoton tsaro na shekarar 2021 da gwamnatin jihar Kaduna ta gabatar dai ya nuna cewa qananan hukumomin Birnin Gwari, Giwa, Igabi, Chikun da Zangon Kataf su ne su ka fi adadin waɗanda ‘yan bindigar suka hallaka a bara.