Mutum huɗu sun mutu kan rikicin N50 a Bayelsa

Daga BASHIR ISAH

Aƙalla mutum huɗu ake fargabar sun mutu a Yenagoa, babban birnin Jihar Bayelsa, sakamakon jayayyar da ta ɓarke tsakanin direban adaidaita-sahu da wani fasinja.

Majiyarmu ta ce jayayyar ta soma ne bayan da fasinja ya miƙa wa direban keken N100 bayan da ya kai inda zai sauka, yayin da direban ya ce kuɗinsa N150 ne, wato dai a yi masa ƙarin N50.

Lamarin da aka ce daga bisani ya rikiɗe ya zama dambe tsakanin fansinja da direban.

An ce, ana tsaka da bai wa hamata iska ne sai direban ya daɓa wa fasinjan wuƙa wanda hakan ya yi sanadiyar mutuwarsa.

Majiyar ta ci gaba da cewa, ganin abin da ya faru ya sa fusatattun matasan yankin suka yi wa direban keken rajamu har lahira

Daga na aka ce rikicin ya rikiɗe ya zama tsakanin ƙabilun yankin na Yenizue-Epie da Hausawa mazauna yankin, lamarin da ya yi sanadiyar samun ƙarin waɗanda suka mutu.

Ya zuwa haɗa wannan rahoto, Gwamnan Bayelsa, Douye Diri, ya kira taro tsakanin shugabannin Yenizue-Epie da na Hausawa mazauna yankin.

Kwamishinan ‘Yan Sanda na Jihar Bayelsa, ya tabbatar da aukuwar lamarin kamar yadda yake ƙunshe cikin sanarwar da Kakakin ‘yan sandan jihar, Asinim Butswat, ya fitar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *