Na sha tunanin kashe kaina, don baƙin cikin rayuwa – Maryam Isa

“Iyayena ne babban ƙalubalena a rayuwa”

Daga ABBA ABUBAKAR YAKUBU

Tarbiyya aba ce mai matuƙar wahalar gaske da ke buƙatar jajircewa, hikima da ƙarfin zuciya. Manazarta na ganin ba kowanne uba ko uwa ne suke iya ɗaukar nauyin iyali ko ba da tarbiyya yadda ya kamata ba, saboda gazawar wasu iyayen wajen laƙantar dabarun tarbiyya da kula da rayuwar yaransu. Wasu iyayen da waɗanda ake bai wa alhakin riqon yara su kansu suna buƙatar kulawa da tarbiyya, bisa lura da yadda suke tafiyar da rayuwarsu ko sauke nauyin da ke kansu. Maryam Isa Ahmad wata matashiya ce da ke zaune a Jos wacce kuma ta taso cikin wani irin rikitaccen yanayi sakamakon fargaba da tsoron da iyayenta suke da shi a game da makomar rayuwarta, kasancewar ta mace, wanda hakan ya jefa ta cikin mawuyacin yanayi da tunanin kashe kanta, saboda tsangwama da rashin yarda da ake nuna mata a gida, duk kuwa da tsantseni da kiyayewar da ta ce tana yi, wajen kare mutuncinta. Wakilin Blueprint Manhaja Abba Abubakar Yakubu, ya samu zantawa da ita, domin jin yanayin da ta samu kanta a ciki da kuma jarumtar da ta nuna wajen jurewar jarrabawar rayuwa da ta ke fuskanta. Ga yadda tattaunawar su ta kasance:

BLUEPRINT MANHAJA: Ko za ki gabatar mana da kanki?
MARYAM: To, ni dai sunana Maryam Isa Ahmad. Ni matashiya ce mai ƙoƙarin neman ilimi da samun madogara a rayuwa. A Jos na ke zaune, kuma a nan na yi karatu da sauran harkokina na rayuwa.

Za mu so mu ji tarihin rayuwarki a taƙaice?
Tarihin rayuwata ba wani mai tsayi ba ne, amma yana cike da darussa masu yawa da kuma ƙalubale iri-iri. Zan iya cewa na kasance ‘ya ta farko a wajen mahaifana. Mahaifina tsohon malamin makaranta ne. An haifeni ba daɗewa mahaifina ya tafi makarantar sojoji domin ya daɗe yana nema. A shekarar 2005 ya gama, sannan aka tura shi aiki Jihar Sakkwato, daga bisani ya ɗauke mu daga Jos mu ka koma zama tare da shi, ni da ƙannaina uku. A lokacin mun yi rayuwa cikin aminci ni da iyayena. Mahaifinmu na sona kuma yana nuna mana kulawa, kamar yadda kowanne mahaifi ya kamata ya nunawa iyalin sa. Bayan kamar shekaru 6 a 2012 mu ka dawo Jos, inda mu ka ci gaba da rayuwa.

Tun bayan dawowar mu gida Jos, sai abubuwa suka fara sauya min, sakamakon sa ido da takurawa da iyayena da ‘yan’uwan mahaifina suka shiga nuna min, saboda ganin na fara girma. Su a wajen su suna min haka ne, don kar na lalace. Alhalin ba su san illar da hakan ya yi wa tunanina da rayuwata ba. Na shiga ƙunci matuƙa, saboda halin da na tsinci kaina, na rashin samun yarda daga makusanta na, tsangwama da yawan zargi. Ni kuma har ga Allah ban taɓa aikata wani abu da bai dace ba, ko biyewa wani ko wata ya vata min tarbiyya ba.
Amma idan ka ga abubuwan da ake min ko ake gaya min a gabana, sai ka ɗauka wata mummunan rayuwa na ke yi ko gagara.

Ko makaranta na je sai a riƙa zargin Ina bin maza, idan kuma wani kuɗi ake buƙata a makaranta shi ma ba a yarda, sai an je har makarantar an bincika. Ballantana a ganni da wani namiji a tsaye mu na magana, babu irin maganar da ba za a gaya min ba. Sai ka ji ana cewa, Ina tsayawa da ýan iska. Har sai da na fara tsargar kaina, Ina tunanin ko ba iyayena ne suka haife ni ba.

Wanne abu ne ya taɓa zama miki babban ƙalubale a rayuwarki?
Wannan rayuwar da na samu kaina a ciki ita ce babban ƙalubalen da na fuskanta a rayuwata. Babu kyakkyawar fahimta tsakanina da iyayena. Sannan ga yawan zarge zarge da baƙaƙen kalamai da na ke fuskanta cikin gida da waje.

Yaya ki ka iya tunkarar damuwoyin da suka dabaibaye rayuwarki?
Addu’a! Addu’a ce ta kasance babban abin dogaro na da samun sanyi a zuciyata. Na san babu abin da zan iya yi in canza tunanin iyayena a kaina, don na jarraba yin hakan sau da dama, amma babu abin da ya canza. Na san duk tsanar da aka yi min ba zai tava yin wani tabo da za a gani a jikina ba. Don haka sai na miƙa wa Allah duk damuwoyina.

Wanne ƙoƙari ki ka yi na ganin kun samu kyakkyawar fahimta da sauran ýan’uwanki na gida, domin sauƙaƙa miki halin da ki ke fuskanta a rayuwarki?
Kamar yadda na sanar da kai a baya, duk ƙoƙarin da ya kamata in yi na yin magana da iyayena, bai canza komai ba. Haka na yi ta fama da muzgunawa daga wajen mahaifina da ƙanin mahaifina da kuma kishiyar mahaifiyata. Sannan ga raini da na riƙa fuskanta daga ƙannaina.

An ce kina rubuta waƙoƙi, wanne salon waƙa ki ke yi?
Ƙwarai ina rubuta waƙoƙi na hip hop Hausa da Turanci, kuma sun ƙunshi maganganu masu yaƙar baƙin ciki da ƙarfafa gwiwar masu sauraro.

To, dama kin gaji waƙa ne a danginki ko haka kawai ki ka tsinci kanki a matsayin mawaƙiya?
To, ai su irin waƙoƙi na yanzu da matasa ke yi, musamman na Hip Hop, ana yin su ne kawai don sha’awa da kuma isar da saƙo. Ba lallai sai wanda ya gaji waƙa daga gidan su ba, don haka nima ba wai gada na yi ba, kalmomin baka na ke yi, musamman a lokacin da na ke cikin wata damuwa ko ɓacin rai. A cikin waƙar na ke faɗin danuwoyina, sai na furzar da abin da ke raina ne na ke jin daɗi.

Ban da waqa wanne abu ki ke yi wanda yake ɗauke hankalinki daga damuwa?
Ina yin zane zane na kayan ɗinki da kuma rubutu shi ma yana ɗebe min kewa, yana kuma sani nishaɗi kwarai. Idan na samu wasu kuɗaɗe kuma Ina amfani da su wajen ɗinka abin da na zana.

Wanne ƙalubale ki ke ganin ýaýa mata na fuskanta daga gidajen iyayensu ko daga mu’amalar su a waje, wanda yake zama matsala a rayuwarsu?
A ganina ƙalubalen da suke fuskanta shine, rashin samun wanda zai saurari damuwarsu, ko ya ba su shawara, ya kuma taimaka musu a rayuwa, ba tare da ya yi musu wata gurguwar fahimta ko ya nemi su yi masa wani abu ko lalata da su ba. ‘Ya’ya mata suna buƙatar tattali da kulawa sosai.

Wanne darasi rayuwa ta koya miki?
Na koyi haƙuri, juriya, rayuwa cikin ƙunci, yaƙar kowacce irin damuwa da ta fuskanto ni. Nuna ƙwarin gwiwa wajen riƙe murmushi a fuskata da danne harshena daga kalaman da ba su dace ba.

Yaya ki ke ganin ya dace gwamnati da masu ilimi su taimaka wa mutanen da suka samu kansu a halin ƙunci da karayar zuciya?

Taimakon da na ke gani ya dace a riqa tallafawa waɗanda suka fuskanci ƙalubalen rayuwa shine, a samar musu da yanayin da za su fahimci cewa rayuwa za ta iya yi musu kyau, kuma akwai wasu da za su iya kama hannunsu su tsallakar da su daga sarƙaƙiyar rayuwa. A kuma samar musu wani jari da zai sa su iya dogara da kansu, wanda hakan zai iya ɗauke tunanin lsu daga halin ƙunci da karayar zuciya da suke fuskanta. Kuma su samu ƙwararru masana ilimin halayyar ɗan Adam da za su taimaka su dawo da kwarjini su ka ƙwarin gwiwar su a rayuwa.

Kin taɓa tunanin kashe kanki saboda halin da ki ka samu kanki a ciki?
Ba sau ɗaya ba, ba sau biyu ba, na sha tunanin in kashe kaina, don in huta da baƙin cikin rayuwa. Na sha kulle kaina a ɗaki na tsawon lokaci, ba ci ba sha saboda baƙin ciki da takaicin rayuwa.

Wanne abu ne ya fi faranta miki rai ko ɓata miki?
Kyauta na faranta min rai, saboda yana nuna min da akwai sauran wasu masu sona. Abin da kuma ya fi ɓata min rai shine, cin amana da kuma ƙarya.

Wanne yanayi ne ya fi sa miki natsuwa a zuciyarki?
Zuciyata ba ta samun natsuwa sai lokacin da na sa ƙafata na fita daga gida, to, a wannan lokacin na ke samun natsuwa.

Wacce karin magana ce ta ke tasiri a rayuwarki?
Mai haƙuri ya kan dafa dutse har ya sha romonsa!

To, na gode.
Madalla. Ni ma na gode.