NBC ta yanke wa Tashar Channels tarar N5m kan saɓa ƙa’idar aiki

Daga BASHIR ISAH

Hukumar Kula da Gidajen Rediyo da Talabiji (NBC) ta ci Tshar Channels tarar Naira miliyan 5 saboda saɓa ƙa’idar aiki.

NBS ta kama tashar da laifi ne yayin wani shirin da ta yi tare da ɗan takarar Mataimakin Shugaban Ƙasa na Jam’iyyar Labour, Dr Datti Baba-Ahmed a ranar Karaba, 22 ga Maris.

Tarar na ƙunshe ne cikin wasiƙar da hukumar ta aike wa Shugaban tashar ta Channels mai ɗauke da kwanan wata 27 ha Maris wadda Kamfanin Dillancin Labarai na Nijeriya (NAN) ya samu leƙawa a ranar Juma’a a Abuja.

Darakta Janar na NBC, Balarabe Ilelah, shi ne ya rattaba wa wasiƙar hannu.

A cikin wasiƙar, Ilelah ya ce “Dr Baba-Ahmed ya ce, saɓa doka ne idan aka rantsar da zaɓaɓɓen Shugaban Ƙasa a ranar 29 ga Mayu, 2023 saboda matsalolin zaɓe.”

Don haka ya ce an saɓa dokar NBC, saboda kalaman Baba-Ahmed na iya haddasa rashin lumana a cikin al’umma.

Ilelah ya ƙara da cewa, sau da dama NBC ta yi jan hankali ga Tashar Channels a kan ta zamo mai lura da buƙatun al’umma wajen gabatar da shirye-shiryenta.

Ya ce Hukumar ta yanke wannan hukunci ne domin taka wa tashar burki wajen ci gaba da yi wa dokokin NBC karan tsaye da kuma jefa ƙasa cikin wani hali.

“Bisa saɓar dokar da Tashar Channels ta yi, an yanke mata tarar N5,000,000…,” in ji shi.