NDLEA ta kuɓutar da yara 34 da aka yi safarar su daga Arewa zuwa Kudu

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Hukumar Hana Sha da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi ta Nijeriya NDLEA ta kuɓutar da wasu ƙananan yara 34 a kan babbar hanyar Okene zuwa Lokoja a jihar Kogi.

Kakakin hukumar, Femi Babafemi shine ya tabbatar da faruwar lamarin a wata sanarwa da ya fitar, sanarwar ta kuma bayyana cewa hukumar ta ƙwace sassan ƙarafunan bindiga a jihar Anambara.

A cewar sanarwar, yaran da hakumar ta kuɓutar sun kasance tsakanin shekaru 8 zuwa shekara 14, waɗanda aka yi safararsu ba bisa ƙa’ida ba daga jihar Ogun zuwa birnin tarayya Abuja.

Ya ce da fari an yi safarar yaran daga jihar Filato zuwa jihar Ondo, inda daga nan ne aka kacancana su gida-gida a matsayin ‘yan aikatau.

Da yake jawabi, shugaban hukumar Birgediya Janar Buba Marwa (mai ritaya), ya jinjina wa tawagar jami’an hukumar bisa aiki tuƙuru da kuma haɗin kan da aka samu tsakaninsu da sauran jami’an tsaro wajen yaƙi da matsalar tsaro a fannin su.

Kazalika Buba Marwa ya bada umarnin mayar da yara 34 da aka yi safara su zuwa Hukumar Yaƙi da Safarar Mutane ta Ƙasa (NAPTIP) domin ɗaukar mataki na gaba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *