Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
A ranar Laraba ne Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ya ƙaddamar da wani sabon shiri na ci gaban ƙasa na dogon lokaci mai taken Nijeriya Agenda 2050 (NA 2050).
Shirin dai shi ne tabbatar da cewa ƙasar na samun GDP na kowace Dalar Amurka 33,328 a duk shekara, wanda zai sanya ta cikin manyan ƙasashe masu matsakaicin larfin tattalin arziki a duniya nan da shekarar 2050.
Shugaban ya ƙaddamar da NA 2050 kafin a fara taron majalisar zartarwa ta tarayya a zauren majalisar da ke Fadar Shugaban Ƙasa a Villa, Abuja.
Ya ce, shirin yana da hangen nesa na bunƙasar tattalin arziki, ci gaban masana’antu da ilimi wanda ke samar da ci gaba mai haɗe da ɗorewa ga ƙasa.
Ya qara da cewa, bisa la’akari da matakan da aka ɗauka na ci gaba da aiwatar da tsare-tsare, gwamnatocin da suka shuɗe za su samu daftarin da zai yi amfani wajen cika alƙawuran zaɓe.
Buhari ya ce, ”Za ku iya tuna cewa a watan Maris, 2020, na amince da samar da tsare-tsare masu zuwa ga Nijeriya Vision 20:2020 da shirin farfaɗo da tattalin arzikin kasa (ERGP), 2017-2020. Tsare-tsaren sun qare a watan Disamba, 2020.
“Don tabbatar da wannan amincewa, na ƙaddamar da kwamitin gudanarwa na ƙasa a watan Satumba, 2020 ƙarƙashin jagorancin Ministan Kuɗi, Kasafi da Tsare-Tsare na Ƙasa kuma fitaccen mai kula da kamfanoni masu zaman kansu, Mista Atedo Peterside.
“Kwamitin gudanarwa shine zai kula da shirye-shiryen ajandar Nijeriya 2050 da shirin ci gaban ƙasa (NDP), 2021-2025 don cin nasara kan shirin Nijeriya na 20: 2020 da shirin farfaɗo da tattalin arziki da ci gaban (ERGP), 2017-2020, bi da bi.
“A wajen ƙaddamarwar, na umarci kwamitin gudanarwar da ya shirya tsare-tsare masu haɗe da juna waɗanda za su shafi dukkanin ra’ayoyi tare da tabbatar da daidaito, tare da samar da dokokin da suka dace don ci gaba da aiwatar da tsare-tsare ko da bayan karewar wa’adin gwamnatin tarayya da gwamnatoci masu zuwa.
‘’An cimma hakan ne tare da shirya kundin na uku na NDP da ke magana da muhimman majalisun dokoki don gano matsalolin da suka shafi aiwatar da tsare-tsare a Nijeriya.
“Yana da kyau in sanar da majalisar da kuma duk ‘yan Nijeriya cewa a ranar 22 ga Disamba, 2021 na ƙaddamar da shirin farko daga cikin tsare-tsare na matsakaicin shekaru shida na 5, shirin ci gaban ƙasa (NDP), 2021-2025, wanda za a yi amfani da shi don aiwatar da Tsarin Dogon Lokaci.
‘’Majalisar kuma a ranar 15 ga Maris, 2023 ta amince da ajandar Nijeriya 2050 da muke qaddamarwa a yau,” inji shi.
Da yake yaba wa kwamitin gudanarwa na ƙasa ƙarƙashin jagorancin ministar kuɗi, kasafin kuɗi da tsare-tsare ta ƙasa, Zainab Ahmed da qaramin ministar kasafi da tsare-tsare ta ƙasa Prince Clem Agba bisa sake gabatar da wannan muhimmin aiki na ƙasa, shugaban ya bayyana da kuma gabatar da jama’a na NA 2050 a matsayin wani muhimmin ci gaba a cikin” tarihin ƙwarewar tsarawa, bayan samun ‘yancin kai”.
Ya ƙara da cewa wannan aikin ya kuma nuna himmar da hukumar ke da shi na tsarawa da aiwatar da tsare-tsare tun lokacin da aka shiga ofis a ranar 29 ga Mayu, 2015.
Dangane da tsarin shirye-shiryen, Ministan Kuɗi ta bayyana cewa ba wai kawai na haɗa kai ne da tuntuɓa ba amma ya haɗa da; wanda ya shafi dukkan masu ruwa da tsaki kamar, dukkan ma’aikatun tarayya, ma’aikatu da hukumomi (MDAs), jihohi 36 da babban birnin tarayya da kuma wakilan ƙananan hukumomi (LGAs).
Ta lissafta sauran masu ruwa da tsaki a matsayin Ƙungiyoyin Masu Zaman Kansu, ƙungiyoyin matasa, ƙungiyoyin ƙwadago, cibiyoyin gargajiya da na addini, manyan jam’iyyun siyasa, ƙungiyoyin mata, masu buƙata ta musamman, da sauransu.
‘’Ajandar Nijeriya ta 2050 an tsara shi ne a kan koma bayan matsalolin tattalin arziki da zamantakewar da ake fama da su a ƙasar, waɗanda suka haɗa da ci gaban ƙasa mara ƙarfi, maras ƙarfi da rashin daidaituwa, rashin tsaro, haɓakar yawan jama’a, ƙarancin rarrabuwar kawuna na tattalin arziƙi da ƙarancin samarwa.
”Shirin wani tsari ne na sauya fasalin tattalin arziki na dogon lokaci da aka tsara don magance waɗannan ƙalubalen,” inji ta.
Ahmed ta kuma shaida wa Shugaban Ƙasa da sauran mambobin FEC da suka halarci bikin ƙaddamarwar cewa, tare da hasashen samun ingantaccen jari, ana sa ran zuba jari a matsayin rabon GDP zai ƙaru daga kashi 29.40 na yanzu zuwa kashi 40.11 cikin 100 nan da shekarar 2050.
Ta bayyana cewa a ƙarƙashin shirin, ana sa ran kamfanoni masu zaman kansu ne za su ɗauki nauyin zuba jarin, yayin da ake sa ran za a samu ƙaruwar ayyukan yi zuwa miliyan 203.41 a shekarar 2050 daga miliyan 46.49 a shekarar 2020.
“Wannan yana nuna rashin aikin yi zai ragu matuƙa zuwa kashi 6.3 a shekarar 2050 daga kashi 33.3 cikin 100 a shekarar 2020. Babban abin da ke nuni da cewa yawan masu fama da talauci zai ragu zuwa kashi 2.1 cikin 100 nan da shekarar 2050 daga miliyan 83 a shekarar 2020,” Ministan ya ce.