Nnamdi Kanu ya sake faɗawa komar Gwamnatin Nijeriya

Daga AISHA ASAS

Gwamnatin Nijeriya ta sake cafke jagoran masu rajin kafa Biafra (IPOB), Nnamdi Kanu.

Bayanai sun nuna an samu nasarar cafke Kanu ne albarkacin wani aikin haɗin gwiwa da aka yi tsakanin Nijeriya da hukumomin tsaron ƙetare.

Kafin wannan lokaci dai, Nijeriya ta shafe shekaru biyu tana neman Nnamdi Kanu ruwa a jallo inda ya tsare neman mafaka a ƙetare.

Babbabn lauyan Nijeriya kuma Ministan Shari’a, Abubakar Malami, ya tabbatar da kama Nnamdi Kanu a ranar Talata yayin wani taron manema labarai na gaggawa da ya gudana a ofishinsa da ke Abuja.

Kanu wanda ke fuskantar shari’a kan laifin ta’addanci da fitinar ‘yan ƙasa da ɗaukar nauyin gudanar da haramtacciyar ƙungiya, ya tsere zuwa ƙetare ne bayan da aka ba da belin shi a wata babbar kotun Abuja.

Alƙali Binta Nyako wadda ita ce ta ba da belin Kanu a ranar 28 ga Maris, 2019 bisa dalili na rashin lafiya, daga baya ta janye belin tare da bada damar a kamo shi duk inda aka gan shi a sassan Nijeriya.

Malami ya ce Kanu zai bayyana gaban Babbar Kotu don ci gaba da shari’arsa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *