NNPP ta buga ɗan gidan Ganduje da ƙasa, ta lashe zaɓen ɗan majalisa a Kano

Daga AMINA YUSUF ALI

Abba Abdullahi Umar Ganduje, ɗa a gurin Gwamnan Jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje, ya faɗi zaɓen ɗan majalisar wakilai a Kano.

Ɗan gidan gwamnan wanda ya fito takarar ɗan majalisar tarayya mai wakiltar mazaɓun Tofa da Rimingado, ya sha ƙasa bayan da abokin karawarsa Tijjani Abudlkadir Jove, ɗan takarar jam’iyyar NNPP ya buga ahi da ƙasa.

Jove wanda shi ne wakilin riƙon ƙwarya na wakilcin majalisar, zai maimaita kujerar tasa ne a karo na biyar.

An kaɗa wa Jove ƙuri’u 52, 456 yayin da Abba Ganduje shi kuma ya samu ƙuri’u 44,809.