PDP ta janye dakatarwar da ta yi wa wasu ƙusoshinta

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

Kwamitin Gudanarwa na Jam’iyyar PDP na Ƙasa (NWC) a ranar jiya Alhamis, ta janye dakatarwar da ta yi wa wasu jiga-jiganta.

Mambobin da aka soke dakatarwarsu sun haza da tsohon gwamnan jihar Ekiti, Ayodele Fayose; Tsohon sakataren gwamnatin tarayya, Anyim Pius Anyim; Farfesa Dennis Ityavyar, Dakta Aslam Aliyu da Ibrahim Shema.

Hakan na cikin wata sanarwar ne mai ɗauke da sa hannun sakataren watsa labarai na jam’iyyar na ƙasa, Debo Ologunaba.

Ya ce, an ɗauki matakin hakan ne yayin taron na NWC a ranar Alhamis, inda mamabobin jam’iyyar suka yi tattaunawa mai zurfi kan abubuwan da ke faruwa a jam’iyyar a baya-bayan nan.

Sanarwar ta ce, “wannan matakin bai shafi ikon NWC na ɗaukar matakin ladabtarwa a kan duk wani ɗan jam’iyya ba a kowanne lokaci bisa tsarin Kundin Tsarin Mulkin jam’iyyar PDP (kamar yadda aka yi wa kwaskwarima a shekara ta 2017).

“NWC ta buƙaci dukkan shugabanni, masu ruwa da tsaki da ’yan jam’iyya su riqa amfani da Kundin Tsarin Mulkin PDP (kamar yadda aka gyara a 2017) da kuma sabon buƙatar haɗin kai da sulhu a jam’iyyarmu a wannan lokacin mai muhimmanci.

“Ya zama dole PDP ta mayar da hankali a yayin da muke ɗaukar duk matakin da ya dace don kwato nasarar da ’yan Nijeriya suka ba wa jam’iyyarmu da ɗan takarar shugaban ƙasarmu, Atiku Abubakar, a zaɓen ranar Asabar 25 da watan Fabrairun 2023 a kotun zaɓe.”

NWC ɗin ta kuma ƙara da cewa, yana da muhimmanci a yi sulhu a tsakanin shugabannin jam’iyyar domin amfaninsu da ‘yan Nijeriya.

Haka zalika, NWC ɗin ta soke miƙa wa gwamnan Benuwai, Samuel Ortom kwamitin ladabtarwa na qasa da ta yi a baya.