Raɗɗa ya zama Gwamnan Katsina mai jiran gado

Daga BASHIR ISAH

Hukumar Zaɓe, INEC, ta ayyana ɗan takarar gwamnan na jam’iyyar APC a Jihar Katsina, Dr. Dikko Radda, a matsayin wanda ya lashe zaɓen gwamnan jihar a zaɓen da ya gudana ranar Asabar.

Raɗɗa ya kai bantensa a zaɓen ne bayan da ya samu ƙuri’u 859,892 wanda hakan ya ba shi damar doke abokin hamayyarsa na PDP, Sanata Yakubu Lado Ɗanmarke, wanda ya samu ƙuri’u 486,620.

Baturen zaɓen kuma Mataimakin Shugaban Jami’ar Tarayya da ke Gusau, Farfesa Mu’azu Gusau ne ya bayyana Raɗɗa a matsayin gwamnan Katsina mai jiran gado.