Ranar Dimukuraɗiyya: Gwamnati ta bayyana 14 ga Yuni hutun gama-gari

Daga BASHIR ISAH

Gwamnatin Tarayya ta bayyana ranar Litinin, 14 ga Yuni, 2021 a matsayin ranar hutun ma’aikata na gama-gari albarkacin bikin ‘Ranar Dimukuraɗiyya’ na bana.

Ministan Harkokin Cikin Gida, Ogbeni Rauf Aregbesola, shi ne ya bayyana haka a ranar Alhamis a madadin Gwamnatin Tarayya. Tare da yin amfani da wannan dama wajen taya ‘yan Nijeriya murnar wannan biki, kana ya yi kira ga ‘yan ƙasa da a ci gaba da mara wa gwamnati mai ci baya domin tabbatar da haɗin kai da cigaban ƙasa.

Aregbesola ya ce al’umma su yi fatali da duk wani nau’i na barazana ga ƙasa don zaman lafiya da amfanin ‘yan ƙasa. Ya ci gaba da cewa Nijeriya za ta ci gaba da zama ƙasa mai zaman lafiya da haɗin kai da kuma cigaban dukkan ‘ya’yanta.

A cewarsa, “Yayin da muke bikin zagayowar Ranar Dimukuraɗiyya a tarihin ƙasarmu, ya kamata mu waiwaya sannan mu dubi irin ƙokarin da magabatanmu suka yi wa ƙasa, kana mu tabbatar da cewa Nijeriya ta ci gaba da zama ƙasa guda dunƙulalliya. Cigaba ba zai taɓa samuwa a wurin da babu zaman lafiya da haɗin kai ba.

“Duba da irin ƙalubalan da muke fuskanta yau a Nijeriya, na hararo dama a gare mu ta mu so juna da gaskiya maimakon rarrabuwa, ta yadda za mu fahimci juna, mu girmama juna sannan mu zauna lafiya da junanmu.

Ministan ya bai wa ‘yan Nijeriya tabbacin cewa, bisa la’akari da irin ƙoƙarin da gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari ke yi na kare rayuka da dukiyoyin ‘yan ƙasa da daidaita tattalin arziki, ƙasarmu za ta ci gaba da samu tagomashi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *