Rayuwar yara na da muhimmanci ga cigaban ƙasar nan

Daga ABBA ABUBAKAR YAKUBU

A wannan makon mai ƙarewa ne aka gudanar da bikin ranar yara ta Afirka, wacce ta mayar da hankali wajen duba halin rayuwar da yara a sassa daban-daban na nahiyar ke ciki, da kuma tattauna hanyoyin da za a bi don kyautata rayuwar su da yadda goben su za ta kasance, a matsayin su na yara manyan gobe.

Na yi wannan rubutu ne domin yabawa da gudunmawar da iyaye ke bayarwa ga tarbiyyar yaran su da ƙalubalen da tarbiyyar iyali ke fuskanta a wannan zamani namu.

Ban san yanzu ko su wa suka fi yawan kaiwa da komowa da rashin samun zama a tsakanin manya da yara, ko kuma iyaye da ’ya’yansu ba. Kowannen su kusan za ka samu akwai matsalolin da suka sha masa kai, da har ya ke ganin ba shi da lokacin da zai zauna da ɗaya daga cikin su. Mafi yawancin iyaye yanzu ba su da lokacin da za su zauna su tattauna da yaran su. Haka su ma yaran ba sa iya samun damar kusantar iyayensu da wata magana da ta shafe su, kai tsaye.

A shekarun baya can zamanin hankali na kwance, yara basu san wai su fita su nemi kuɗi a waje ba, ko kuma a tura su koyon sana’a ba. Hatta iyayensu mata ma basu damu da yin wani abin sayarwa a gida ba. Duk iyali sun dogara ne da abin da Uba ko Maigida zai shigo da shi gida daga waje. Kuma daidai gwargwardo ana samun biyan buƙata da rufin asiri. Yanzu kuwa rayuwa ta canja nesa ba kusa ba.

Talauci da wahalhalun rayuwa sun tarwatsa iyalai da dama, an fantsama neman abin duniya. Akasarin magidanta tun sassafe sun fita kasuwa ko neman na cefane, wasu daga cikin su basa kara waiwayar gida sai dare ya yi. Su kan su yaran daga sun taso makaranta, musamman masu ɗan wayo, sai ka ga suma sun bazama nema, daga masu zuwa sana’a, koyon aiki, sai masu karan-mota. Sam basu ma da lokacin da za su zauna su huta a gida, ko kuma su ɗauki littattafansu domin yin bita.

Yanzu an kai wani lokaci da wasu yaran ne ma suke ɗaukar ɗawainiyar gidajen su, ta hanyar ragewa iyayen su wasu ’yan nauye-nauyen. Amma duk da halin da ake ciki, yana da matukar muhimmanci iyaye su samar da wani lokaci na musamman da za su dinga kusantar iyalinsu, suna hira ta raha da nishadantarwa domin ƙarin samun shaƙuwa da fahimtar juna.

Ya kamata ku yi wa yaranku wasa da dariya, ku saki jiki da su yadda za su kusanceku su yi maku ɗa’a da biyayya. Ba lallai sai kun zauna kun wuni a gida ko kun ware masu rana ta musamman ba. Amma dai a ƙalla a ce kun samu lokacin da za ku ci abinci tare, ko da ba a kwano ɗaya ba, ya zama dai a muhalli ɗaya. Haka nan idan dare ya yi kafin su yi barci, nan ma lokaci ne mai kyau na hira da iyali. Fita da su unguwa, ko zuwa wuraren shaƙatawa, zuwa ziyarar ’yan uwa da abokan arziki, yana qara shaƙuwa sosai.

Idan da za ku samu lokaci ku zauna kuna kallon talabijin tare ko irin finafinan nan na Hausa masu ma’ana, nan ma wata dama ce da za ka yi amfani da ita ka faɗakar da su abubuwan da ya kamata su kiyaye game da zaman duniya.

Zama da su lokacin da ka ke cikin bacin rai, zai basu damar gane yadda ake haɗiye fushi da dauriya. Sannan fara’a da wasan zolaya yayin da ake cikin farin ciki zai ƙara masu sakewa cikin nishaɗi. Ko ba ka furta komai ba, kallo kawai ko murmushi, ko tavawa ya wadatar da ya nuna irin abin da ke zuciyarka game da su.

Nunawa yara yadda za su dinga ɗaukar kansu yana da matuƙar muhammanci, domin yana taimaka masu wajen ƙarin kuzari da cikakkiyar lafiya. Yaran da ake kula da rayuwarsu sosai, sun fi samun sakamako mai kyau a jarabawar makaranta.

Yana da kyau iyaye su rinka zuga yaransu da kalamai masu ƙarfafa gwiwa, don su kara zakewa da mayar da hankali a sha’anin karatunsu. Amma ba ta yadda za su riƙa alfahari da girman kai ba.

Akwai iyaye da dama da suke cikin takaici na lalacewar tarbiyyar yaransu ko dai ’yar su na bin ’yan iskan samari ko lalatattun ƙawaye, ko kuma ɗan su ya fara shaye-shaye, ana kuma zarginsa da ’yan ɗauke-ɗauke. Babu wani Uba da zai bugi ƙirjin ’ya’yansa sun wuce wannan hali, ko kuma ya fi ƙarfin a ce sun aikata wani mugun hali. Idan har Allah ya jarabce ka da irin waɗannan yaran to, kana buƙatar ka ƙara jawo su jiki sosai, tare da nuna masu muhimmancin su gyara ɗabi’unsu domin su taimakawa rayuwarsu.

Ka daɗa nuna masu irin son da ka ke masu da burinka na shiryuwarsu, sannan ka dage sosai da addu’a. Wasu yaran duk ƙoƙarin ka babu yadda za ka yi ka canja su, don haka kada ka ɗora damuwa ko laifin kintsuwarsu a kan ka. Hausawa na cewa, “Hali zanen dutse.” Kuma an ce, “Ma ba da hali ya riga mahori.” Ku bari su faɗa maku yadda suke ji a ransu, da kuma abubuwan da ke damunsu. Ku saurari abin da yafi burge su, da wanda ya ke yawan bata masu rai. Hakan zai taimaka muku sosai wajen fahimtar yadda suke kallon abubuwa, da kuma yadda suke tunani, don ku ba su shawarwarin da suka dace.

Komai girmansu yara basa wuce lokacin zama da iyaye. Akwai abubuwa da dama da ke zama har abada a cikin ƙwaƙwalwarsu, na wani ɗan ƙanƙanin lokaci da suka yi wani abu tare da iyayensu. Hatta waɗansu kalmomi da suka ji ko aka faɗa masu game da rayuwa ba kasafai suke mantawa da irin su ba.

Muhimmiyar hanyar da za ka bi ka gyara halayyar yaronka, shine ka fara da kanka, domin ka zamar masu abin koyi, kamar yadda Dr. Ellen Rudolph, masaniya akan rayuwar iyali ta ke cewa, “Yayin da iyaye suka kyautata halayensu da zamantakewarsu, nan da nan yaro zai iya tashi da ɗabi’u nagari irin nasu. Inda aka fi samun matsala shine idan iyaye suka matsa da takurawa da kafawa yaro tsauraran ƙa’idoji, don kada ya lalace. Yawan wa’azi da tsoratarwa ba sune suke tasiri ba, ku zauna da su ku yi masu wasa da dariya.”

Yana da kyau mu sani cewa wasu yaran sun fi wasu shiga rai. Ba laifi ba ne don ka ji zuciyarka ta fi kwantawa da wani daga cikin ’ya’yanka. Domin wani lokaci sai ka ga haka kawai jininka bai haɗu da wani daga cikinsu ba, har ma sai shaiɗan ya fara raya maka a rai cewa, ko ba ɗanka ba ne? Sam ba haka ba ne, shi dai haka Allah ya halicce shi. Kuma ko a cikin mutane idan ka duba za ka ga wasu na da saurin shiga rai, wasu kuma suna da wuyar sha’ani. Yi ƙoƙari ka ga ba ka bayyana irin wannan bambanci a tsakaninsu ba, ka nuna masu matsayinsu ɗaya a wajenka. Kowanne kuma ka bashi haƙƙinsa na soyayya da kulawa ta musamman da ke wuyanka. Akwai wani babban kuskure da wasu iyaye ke yi, wanda ya ke ba ƙaramar cutarwa ya ke a kwakwalwar yara ba. Wannan abu kuwa shine na kwatanta ɗan ka da wani, ko a tsakanin sa’o’i ko abokanai, da kawaye, ko kuma ’yan uwansa na gida. Ba bakon abu ba ne, ka ji uba ko uwa na zargin yaronsu, mai ya sa bai iya kamar wane ba, ko kuma don mai ya sa bai zama kaza ba, da mai wane ya fi shi, rago ne shi malalaci. Waɗannan kalamai ba ƙaramar guba ba ce kuke ɗurawa yara, wanda idan illar su ta tashi har ku sai ta shafa.

Kowanne yaro da yadda Allah yake halittarsa. Yaron da ka ke ɗauka sauna, malalaci, gaba yana iya zama mai kishin zuci da hangen nesa. Shine wanda wata rana zai tallafa maka ya share maka hawaye. Wancan kuma da ka ke tunanin gwarzo ne, yana iya canjawa ya zama gagararre, wanda zai fitine ka. Don haka bambancin halayyar yara da zafin namansu, ko sanyin zuciyarsu, ba shine ya ke nuna abin da za su zama gaba ba. Kowa da irin baiwarsa, bambancin su na iya kasancewa rahama ce gareka. Domin duk idan ka bi su a yadda kowannensu ya ke, zaka tarar da wani abin ban mamaki da ba ka taɓa zato ba, a tare da su.

Yayin da yara suka fara zama matasa, suna son iyayensu su riƙa ɗaukarsu a matsayin manya, ba kamar ƙanana ba. A halin da suke ciki kuma suna matuƙar buƙatar iyayensu su jawo su jiki, don su fahimce su, a riqa shawartarsu a waɗansu al’amura, kuma a nuna masu amincewa. Iyaye su kula da kyau, taurin kai, da rashin tsayawa akan abu ɗaya da wasu matasa kan nuna wani lokaci ba suna yi ne don rashin ladabi ko kuma don rashin kunya ba. A’a, sai dai yanayin halittar da suke ciki a lokacin ne, ya canja. A lokacin suna buqatar ne su fahimci kansu da kansu, su samu ’yancin yin zaɓi a rayuwarsu na abin da suke so.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *