Daga BASHIR ISAH
Tsohon Shugaban Majalisar Dattawan Nijeriya, Dr Bukola Saraki, ya yi zargin an sace Naira tiriliyan 2 a fannin mai ƙarƙashin gwamnatin APC.
Kazalika, Saraki ya yi zargin cewa Nijeriya na fama da fatara kasancewar kamfanin man fetur na ƙasa (NNPC) ba ya bada kowace gudunmawa ga asusun ƙasar (FAAC) a tsakanin ‘yan watannin da suka gabata.
Ya ƙara da cewa, man fetur kimanin lita miliyan 70 ake sacewa duk yini yayin da ƙasar ke hasarar kuɗi Dala biliyan $2 duk shekara ta hanyar maguɗin tallafin fetur.
Saraki ya yi alƙawarin muddin aka zaɓe shi ya zama Shugaban Ƙasa, zai daƙile maguɗi da rashawar da ake tafkawa a fannin mai.
Ɗan siyasar ya yi waɗannan bayanan ne a lokacin da ya gana da Kwamitin Amintattu na jam’iyyar PDP kwanan nan a Abuja.
A cewar Saraki, “Tattalin razikin Nijeriya ya yi rauni. A’a. Fatara ƙasar ke fama da ita. Ba wai ririta zance nake yi ba.
“Ya zuwa yau, NNPC bai bada gudunmawar komai ba ga asusun ƙasa. Kashi 70 cikin ɗari na manmu sacewa ake yi, irin haka bai faru ba a baya.
“Ina wannan zancen ne saboda na san kun san hakan babu kyau, amma lamarin ya ƙazance fiye da yadda kuke tunani. Saboda akwai wasunmu da ke da masaniyar yadda lamarin ya munana.
“Ba zai yiwu ina matsayin Shugaban Ƙasa sannan in bari irin satar da ake tafkawa a yankin Niger Delta ta riƙa faruwa ba, ana hana miliyoyin ‘yan Nijeriya more rayuwa. A yau muna hasarar Dala biliyan $3.5 saboda satar mai.
“A lokacin da nake Sanata na yi wani ƙorafi a majalisa da ya saka ni cikin wani hali, kan cewa abin da aka ce ana kashewa a kan tallafin mai duk ƙarya ne, sai da EFCC ta gayyace a kan haka amma na dake a kan abin da nake faɗa a kansa.
“Na yi ƙorafi a kan muna amfani da litar mai har miliyan 30 kulli yaumi, bayan haka sai abin ya ragu zuwa lita 25. A sakamakon abin da na yi ya sa a yau ake iya tara wa ƙasa Dala miliya $500. A yau suna sace litar mai miliyan 70 duk yini, zan dakatar da ci gaban faruwar hakan muddin aka zaɓe ni shugaban ƙasa, sannan mu hana sace kuɗaɗen ƙasa sama da Naira tiriliyan biyu.
“Kun kuwa san abin da tiriliyan N2 zai yi wa makarantunmu, fannin ilimi da na lafiya? Yanzu ne lokacin da ya kamata mu samu mutumin da ya dace don ya riƙe mana ƙasa.”
Saraki ya ce shi ne mutumin da zai iya fitar da Nijeriya daga cikin halin da ta tsinci kanta a yau muddin dai ‘yan Nijeriya suka ba shi damar da zai mulki ƙasa.