Sharhin fim ɗin ‘Kan Ta Kile’

Daga LAWAN MUHAMMAD PRP

Sunan Fim: Kan Ta Kile
Kamfani: Bahaushiya International Limited
Rubutawa da Tsarawa: Zubairu Musa Balannaji
Shiryawa: Zubairu Musa Balannaji
Umarni: Victor Idrees D Bass
Taurari: Alassan Kwalle, Hajiya Zahra’u Fantami, Auwal Ahmad, Halima Y. Adam, Hamisu Danbirni, Halimat Muhd, Ladidi Tubles, Basira Isah, Hadiza Kabara, Mustafa Karkasara, Husna Khaleed, Safiya Adamu, Hafsat Saraki, Sulaiman Bosho, Rukayya Mohd, Nafisa Ja’en, Salisu Loto, da sauransu.

Gabatarwa:
Kan Ta Kile fim ne mai dogon zango da ya samu shiryawa, labari da tsarawa daga fitaccen matashin Marubuci kuma mashiryin fina-finai Zubairu Musa Balannaji.

Labarin wata yarinya mai suna Sa’ade (Basira Isa) da ta taso cikin tsangwama a gidansu, yayin da kishiyar babarta Inna Safiya (Zahra’u Fantami) da kusan kowa na gidan ya tsane ta in ka ɗauke Wanta Magaji (Hamisu Danbirni) dake nuna mata tausayawa.

Tana da ‘yar uwa Karime wadda ba uwarsu ɗaya ba da ake nunawa so da kulawa.

Ana ɗora wa Sa’ade talla kamar yadda al’adar ƙauyen ta nuna.

Akwai wani matashi da ya nuna yana son Sa’ade amma sai aka je wurin boka, aka jirkita hankalinsa domin soyayyar ta koma kan Karime, bayan sharrin maita da aka liƙa mata har ta kai ta haƙura ta karba duk da tsananin farin jinin da take da shi.

A gefe guda akwai Maigari (Alassan Kwalle) dake son wata yarinya Dije, matarsa (Asma’u Sani) ta gaji da aure-auren da Maigari ke yi, takan bi yarinyar da Maigari ke so ta lakaɗa mata duka, kuma tana samun sirrin mijinta ne a wurin yaronsa Wakili. Akwai samari masu lalata yaran mutane (‘yam mata) irin su Salisu Loto da abokansa, duk da suna wani ɓangare na barkwanci a labarin.

Bangon fim ɗin

Yabo:
An yi ƙoƙarin sarka rigingimu a labarin ta ɓangare daban-dabam don tabbatar da an samu jan hankalin mai kallo. Haka nan yadda ‘yan wasan suka zage suka yi aiki kai ka yi tsammanin ‘yan ƙauyen gaske ne tuburan! 

An yi amfani da kayan aiki masu kyau, haka kuma hoto ya tsaya ba ya rawa, ga alama mai tace fim ɗin (Editor) ya yi aikinsa sosai.

Darakta da sauran ma’aikata sun taka rawa sosai bayan gwanintar da jaruman labarin suka nuna.

Gyara:

  1. Yanayin labarin ya yi kyau sai dai jaruman da aka zuba sun yi yawa matuqa ta yadda cire wasu daga ciki ba zai ragewa labarin karsashi ba.
  2. Zarurrukan labarin su ma sun yi yawa tamkar jaruman, ta yadda mai kallo yake iya manta wani zaren saboda rashin ba shi muhimmanci ko kuma mantuwa yayin sarka shi da labarin.
  3. Babu tsayayyen jigo a fim ɗin, in ma akwai to bai fito fili ba sosai yana buya a cikin ƙananan jigogin da ba wasu masu armashi ko sababbi ba ne.
  4. Kamar yadda na faɗa, jigon da ya ɓuya ana ta wahalar tsayar da shi, don yana yin rawa a wasu wuraren.
  5. A episode nan10 gurin da Abashe (Sidi Auwal) ya kwacewa wani yaro kuɗin aike bayan yaron ya tafi ya haɗu da Magaji (Hamisu Danbirni) har sun rabu sai ga muryar Darakta ko wani a bayan fage yana cewa yaron “ci gaba da kukanka.”

Har zuwa episode na 11 dai jarumar ba ta ƙile ɗin ba, watakila sai nan gaba ko a season 2 na fim ɗin. Mun ga dai mahaifin Sa’ade ya bayyana a episode na ƙarshe-ƙarshe a season 2.

Rufewa:
Duk da haka dai an yi ƙoƙari wajen ɗaukar fim ɗin, musamman da yake wannan ne fim na farko da mashiryin fim ɗin ya shirya. Mu na fatan nan gaba za a duba kurakuran da aka samu, don gyarawa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *