Shugaba Buhari ya aika da saƙo ga kocin Super Eagles

Daga WAKILINMU

Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ya buƙaci kocin Super Eagles, Austin Eguavoen da ya ci gaba da kuma zarce yadda ya kai ga nasara a gasar cin kofin Afrika (AFCON) da ake yi a Kamaru.

A cikin wata sanarwa da ya fitar a daren Larabar da ta gabata ta hannun mai ba shi shawara na musamman kan harkokin yaɗa labarai Femi Adesina, Buhari ya bayyana cewa ƙasar na fatan samun nasara guda bakwai a gasar.

Shugaba Buhari ya yaba wa ƙungiyar bisa ƙoƙarinta na lashe dukkan wasanninta na rukuni wanda ya sa ta tsallake zuwa zagaye na biyu a gasar cikin gaggarumin salo.

Shugaban ya bayyana fatansa na cewa, kyawawan wasannin motsa jiki da magoya baya da marubuta wasanni da ƙungiyar ƙwallon ƙafa ke nunawa a ƙasar Kamaru, zai kawo zaman lafiya da ci gaba ga al’ummar ƙasar.

Buhari ya yi wa Super Eagles fatan alheri, inda ya yi alƙawarin cewa gwamnatinsa za ta ci gaba da bayar da goyon baya ga ƙoƙarin ƙungiyoyin ƙwallon ƙafa na ƙasa da ƙasa da na shiyya-shiyya da na ƙasa, a yunƙurinsu na amfani da wasanni a matsayin wani makami na gina duniya mai kyau da kwanciyar hankali.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *